IBB ya mika kokon bara ga 'yan Najeriya dangane da zaben 2019

IBB ya mika kokon bara ga 'yan Najeriya dangane da zaben 2019

- Tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta mika mulki ga matasa

- IBB ya bukaci 'yan Najeriya da su mallaki katin zabe na dun-dun-dun domin su taka muhimmiyar rawa a zaben 2018

- A wata takarda da ya aike ga shugaba Buhari a watan Fabrairu, IBB shawarci Buhari da ya janye jikinsa ya koma gefe domin bawa matasa damar gina Najeriya

Bayan rubuta doguwa wasika ga shugaba Buhari tare da bashi shawarar ya hakura da tsayawa takara a 2019, tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya bukaci 'yan Najeriya da su kada kuri'un su ga matasa kawai a zaben 2019.

Legit.ng ta rawaito cewar IBB na wadannan kalamai ne a gidansa dake Minna dake jihar Neja yayin da ya karbi bakuncin wata kungiyar matasa "YES Nigeria Movement".

IBB ya mika kokon bara ga 'yan Najeriya dangane da zaben 2019
Ibrahim Badamasi Babangida
Asali: Depositphotos

Ya bukaci jagororin kungiyar da suyi amfani da damar zabe da suke da ita a zabe mai zuwa domin cicciba matasa da suka tsaya takara ga nasara.

DUBA WANNAN: Barkewar sabon rikicin kabilanci a jihar Kogi: An kashe mutane 5, an kona gidaje 50

A wata takarda da ya aike ga shugaba Buhari a watan Fabrairu, IBB shawarci Buhari da ya janye jikinsa ya koma gefe domin bawa matasa damar gina Najeriya.

Saidai a wannan karon, IBB kira ya yi da roko ga 'yan Najeriya, musamman matasa, da su mike tsaye domin ganin sun kawo canji a kasa ta hanyar tsayar tare da zabar matasa lokacin zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel