Saboda albarkar Shehu Inyass aka yi ruwa jiya a Kaduna Inji wani ‘Dan ‘Darika
- Wani ‘Dan Darika ya bayyana cewa bikin Shehin Inyas ya sa aka yi ruwan sama
- An dade ana jiran ruwan sama a Garin Kaduna wannan shekara ba a samu ba
- Wannan Bawan Allah yace albarkacin Shehu mai karamomi ne ruwa ya sauka
Mun samu labari cewa wani kasurgumin Mabiyin ‘Dan ‘Darika yayi ikirarin cewa saboda albarkar Sheikh Inyass ne aka samu ruwan sama a Garin Kaduna bayan an dade ana tsammanin saukan ruwan saman amma shiru.
Wannan Bawan Allah mai suna Jibril @Jaybee_am yayi amfani da shafin sa na Tuwita jiya inda yace an dade ana jiran ruwan sama a Kaduna bana ba a samu ba sai bayan da aka fara Mauludin ranar haihuwar Sheikh Inyass a jiya.
KU KARANTA: Jama’a sun yi kira ga Kwankwaso ya fito takara bayan taron Mauludi
Jihar Kaduna dai na cikin Garuruwan da ba ayi ruwan sama ba a wannan shekarar duk da an samu saukar ruwan a Jihohin da ke Makwabtaka da Garin. Malam Jibril yace tabarrukin Shehin na ‘Darika ne ya sa ruwa ya sauka a jiya.
Idan ba ku manta ba a jiya ne ‘Yan darikar Tijjaniya su kayi bikin tunawa da babban Shehin su kuma babban Waliyyi Ibrahim Inyass wanda aka haifa a irin wannan lokaci. Ibrahim Inyass ya rasu ne dai shekaru fiye da 40 da su ka wuce.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng