Gwamna Ganduje ya samu babban karamci ta 'Jaruman Kano'
Rahotanni da sanadin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, an yiwa wasu jiga-jigai karamcin lambar yabo ta Jaruman Kano da suka hadar har da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da tsohon ministan ilimi, Mallam Ibrahim Shekarau.
Wannan karamci ya shafi mataimakin shugaban hukumar sadarwa na Najeriya, Farfesa Umar Garba Dambatta, tsohon gwamnan jihar na farko a mulkin farar hula, Marigayi Muhammadu Abubakar Rimi, tsohon gwamna Marigayi Audu Bako, tsohon San Kano Marigayi Mai Martaba Alhaji Ado Bayero tare da aminin sa Marigayi Yusuf Maitama Sule, Danmasanin Kano.
Sauran wanda suka samu wannan lambar yabo sun hadar da; Sarki Kano Muhammadu Sanusi II, Marigayi Janar Murtala Muhammad, kwamishinan Noma na Jihar, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna da kuma Dan-adalan Kano, Alhaji Isyaku Umar Tofa da sauransu.
KARANTA KUMA: Wani Masaki ya fyade 'yan mata 4 a jihar Kebbi
Legit.ng ta fahimci cewa, cibiyar sadarwa da watsa labarai ta Destiny Channel Broadcasting Network ke da ruwa da tsaki na wannan karamci gami da lambar yabo
A yayin ganawa da manema labarai bayan karbar lambar yabon, Farfesa Dambatta ya kirayi matasan Najeriya akan tunkarar duk wani kalubale tare da mayar da hankali akan hanyoyin da za su bunkasa rayuwar su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng