2019: An nemi Sanata Kwankwaso ya tsaya takara a Najeriya
- A Ranar Asabar ne aka yi bukukuwan Mauludi na Sheikh Inyassi
- Rabi’u Kwankwaso ya samu halartar taron a Kaduna da ma Abuja
- Ganin yadda aka tarbi Kwankwaso ne wasu su ka nemi yayi takara
A jiya ne tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya halarci taron mauludin da aka yi a Birnin Tarayya Abuja da kuma Garin Kaduna inda ya kuma ci kasuwa yayin da jama’a su ka cika makil.
Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakin su bayan ganin abin da ya faru a taron inda wata mai suna Ndi Kato (@Yarkafanchan) tace za su yi iya bakin kokarin su na ganin cewa Kwankwaso ya tsaya takarar Shugaban kasa a kowace Jam’iyya ce.
KU KARANTA: Shehin 'Darika yayi magana game da zaben 2019
Shi kuma wani mai suna @Is_salsu cewa yayi bayan Shugaba Muhammadu Buhari babu wani ‘Dan siyasa mai farin jini a kasar nan irin Kwankwaso. @Is_salsu yace bai ga dalilin da zai sa Jam’iyyar APC mai mulki ta ki tsaida Sanata Kwankwaso ba.
Kwanakin baya dama dai Fasto Tunde Bakare wanda su kayi takara tare da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2011 karkashin Jam’iyyar CPC yace ya gano wani ‘Dan Arewa ne zai fito salin-alin ya buge Shugaban kasa Buhari daga kan kujerar sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng