2019: Shehi Dahiru Usman Bauchi ya gargadi mabiyan sa kan yin Katin zabe
Jagoran 'yan darikar Tijjaniya na Najeriya, Shehi Dahiru Usman Bauchi, ya gargadi mabiyan sa akan su tabbatar da yin rajista tare da mallakar katin kada kuri'a kafin gabatowar zaben kasa na 2019.
Babban Shehin ya yi wannan fadakarwa ne a ranar Asabar din da ta gabata yayin bikin maulidi da zikirai na shekara da aka saba gudanarwa wanda kungiyar 'yan darikar ta shirya a babban birnin kasar nan na tarayya.
A cewar Shehu, katin kada kuri'a shine babban makami da al'umma za su rika wajen zaben wanda suke bukatar ya jagoranci al'amurran kasar nan.
KARANTA KUMA: Wani hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 4 da raunata 19 a jihar Kano
Shehu ya kuma kirayi mabiyan sa akan amfani da hikima wajen kada kuri'un su na zaben mutanen da suke da tabbacin gamsar da su gami da biya ma su bukatu domin cikar burika.
Ya kara da cewa, katin kada kuri'u shi zai baiwa daukacin al'ummar kasar nan dama wajen shiga cikin al'amurran gwamnati domin sharbar romon dimokuradiya
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng