Asiri ya tonu: Dakurun soji sun kama wasu da ke da hannu cikin kashe-kashen jihar Taraba
- Dakaru sojin sunyi nasarar damke mutane biyu da ke da hannun cikin kashe-kashe da tayar da fitina a jihar Taraba
- Wadanda aka kama sun hada da Dansabe Gusama da Danjuma wanda akeyiwa lakabi da Dan Amurka
- Sojojin sunyi nasarar kama batagarin biyu ne sakamakon bayyanan sirri da ke nuna cewa sun dade suna kai hare-hare a sassan jihar
Dakarun Sojojin Najeriya wanda ke gudanar da atisayen 'Ayem Akpatuma' sun damke mutane biyu da ke da hannu cikin tayar da rikicin Taraba wanda ya faru a kananan hukumomin Takum da Ussa, wanda aka kamu sune; Danasabe Gasama da kuma Danjuma wanda alkafi sani da Dan Amurka.
Kakakin hukumar Sojin, Brig. Janar Texas Chukwu ne ya bayyana hakana cikin wata sanarwa da ya bayar a yau Asabar.
DUBA WANNAN: Dalilin da yasa har yanzu ba'a ceto 'yan matan Chibok ba - Buhari
Yayi karin bayyani inda yace anyi nasarar kama mutanen biyu ne a Takum sakamakon bayyanan sirri da ke nuna cewa suna da hannu cikin kai hare-hare da dama akan makiyaya da kuma mutanen asalin mutanen yankin.
"Binciken da aka fara gudanarwa ya bayyana cewa mutane biyun nan suna da hannu dumu-dumu cikin kashe-kashe da tashin hankula da ya faru a kananan hukumomin guda biyu.
"Muna bayar da shawara ga al'umma su rika bayar da bayannai masu amfani ga hukumomin tsaro a kan lokaci saboda a rika daukan mataki cikin gagawa", inji Chukwu.
Rahoton da muka samu daga Daily Post ya bayyana cewa a kalla mutane 25 ne suka rasa rayyukansu sakamakon wata sabuwar harin da ake zargin makiyaya ne suka kai a kauyen jandeikyula da ke karamar hukumar Wukari a jihar Taraba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng