Aminu Atiku ya sake daukaka kara bayan kotu ta mallakawa tsohuwar matarsa rikon yayansu

Aminu Atiku ya sake daukaka kara bayan kotu ta mallakawa tsohuwar matarsa rikon yayansu

Aminu Aiku, dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shigar da kara a babban kotun Igbosere a Legas inda yake bukatar kotun ta warware hukuncin da aka yanke a bayan na bawa tsohuwar matarsa rainon yaransu guda biyu.

A ranar 10 ga watan Janairu ne karamar kotun ta baiwa Fatima Bolori ikon rainon yaransu biyu, Ameera mai shekaru 11 da kuma Aamir mai shekaru bakwai.

Bolori da Atiku sunyi aure ne a shekarar 2007 kuma daga bisani auren ya mutu a shekarar 2011 saboda wasu matsaloli da suka gaza warwarewa tsakaninsu.

Dan Atiku yana bukatar kotu ta mallaka masa yara bayan sun rabu da matarsa
Dan Atiku yana bukatar kotu ta mallaka masa yara bayan sun rabu da matarsa

Bayan da karamar kotun ta yanke hukuncin bawa mahaifiyar yaran ikon rainonsu, kotun kuma ta umurci Atiku ya rika biyan N500,000 duk wata saboda kulawa da yaran biyu. Kazalika, kotun ta umurce shi ya samar da isuran lafiya da yaran guda biyu.

DUBA WANNAN: Masana sunyi gargadi kan illolin amfani da wayyar salula da daddare ga dalibai

A yayin da yake magana a jiya Alhamis a kotun, Atiku yayi ikirarin cewa karamar kotun da ta yanke hukunci a baya bata bashi damar bayar da ba'asi ba kafin ta yanke hukuncin mallakar yaran ga tsohuwar matarsa.

Lauyan Atiku, Oyinkan Bodejo ta shaida wa kotu cewa batayi adalci ga wanda take karewa ba saboda ta yanke hukunci ne a ranar da aka ware don sauraron karar kawai.

Bodejo kuma ta kara da cewa nauyin da aka daura wa Atiku yayi masa yawa na biyan N500,000 duk wata ga don kulawa da yaran, ga kudin kula da lafiyarsu da sauran kudin kashewa.

A gefe guda, Lauyoyin Bolori, ON Olabisi da Etherl Okoh sun ki amincewa da rokon da lauyan Atiku tayi inda suka ce lafiyar yaran yana da muhimmanci sosai. Alkalin kotun ya bawa Atiku damar shigar da daukaka karar kuma ya dage sauraon karar zuwa 17 ga watan Mayu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164