Uba da ɗa sun shiga hannun hukuma da laifin lalata da karamar Yarinya

Uba da ɗa sun shiga hannun hukuma da laifin lalata da karamar Yarinya

Wata Kotun Majistire dake zamanta a unguwar Oredo ta birnin Benin dake jihar Edo, ta gurfanar da wani mahaifi ɗan shekara 50, Reuben Enosegbe da ɗan sa Destiny mai shekaru 16 da laifin lalata da wata karamar yarinya 'yar shekaru 10.

Kotu na zargin wannan Reuben da Destiny da aikata laifin yiwa wata karamar yarinya fyade da shekarun ta ba su wuci 10 a duniya ba.

Uba da ɗa sun shiga hannun hukuma da laifin lalata da karamar Yarinya
Uba da ɗa sun shiga hannun hukuma da laifin lalata da karamar Yarinya

A yayin shigar da korafi a gaban kotu, Legit.ng da sanadin jaridar The Punch ta fahimci cewa wannan mutane biyu sun aikata laifin ne a unguwar ta Oredo wanda ya sabawa sashen na 218 karkashin dokokin yankin Bendel da aka kaddamar tun a shekarar 1976.

KARANTA KUMA: Wata Mata ta buƙaci saki sakamakon Mijinta mai yawan jima'i ta Dubura

Rahotanni sun bayyana cewa, har yanzu dai binciken kotun bai ta kama wannan mahaifi da ɗan sa cikin aikata laifin ba, sai dai alkaliyar Kotun Efe Akhere, ta daga sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Afrilu.

Lauya mai kare wadanda ake zargi, Nicholas Omobude, ya nemi kotun da ta bayar da belin su, inda ta hau kujerar naki da cewar hakan ba zai yiwu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng