Mun ga amfanin Gwamnatin Buhari Inji Gwamna Ikpeazu
- Gwamnan Jihar Abia ya bayyana cewa sun ga aikin Gwamnatin Buhari
- Okezie Ikpeazu yace a duk rana sai an ba ‘Yan makaranta a Jihar abinci
- Gwamnan yace an yi wata-da-watanni ana samun wutar lantarki a Abia
Mun ji labari daga Fadar Shugaban kasa cewa Gwamnan Jihar Abia ya yabawa Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a dalilin wasu kokari da Gwamnatin ta ke yi na inganta harkar kasuwanci da kuma ilmin zamani.
A makon nan ne Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara Jihar Abia domin kaddamar da wasu ayyukan Gwamna Okezie Ikpeazu a bangaren kiwon lafiya. Bayan nan Yemi Osinbajo ya wuce Jihar Anambra.
KU KARANTA: Abaribe ya jefa Majalisa cikin hatsaniya da ya soki Buhari
A wajen taron, Gwamna Okezie Ikpeazu ya bayyana cewa Yaran makarantan Firamare a Jihar Abia na samun abinci kyauta a duk rana ta Allah. Gwamnan ya kuma ce an yi kusan watanni 5 kenan ba a dauke wuta ba wasu barayin.
Gwamnatin APC ta kawo wasu tsare-tsare na taimakawa marasa galihu a fadin Najeriya wanda daga ciki akwai ba ‘Daliban makaranta abin karin-kumallo. A jiyan ne dai kuma wani Sanatan na Abia ya soki Gwamnatin Shugaba Buhari.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng