Matsalar tsaro a Kaduna: Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 18 bayan sun kashe Yansanda 2

Matsalar tsaro a Kaduna: Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 18 bayan sun kashe Yansanda 2

Wasu gungun yan bindiga, kuma masu garkuwa da mutane sun kai wani mummunan hari a karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna, inda suka bindige yansandan guda biyu da sace mutane goma sha takwas.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito yan bindigan sun kai wannan hari ne a ranar Alhamis 12 ga watan Afrilu, a wani shningen binciken ababen hawa da jami’an Yansanda suka sanya a kauyen Ciki da falo na garin.

KU KARANTA: Jarabawar gwaji: Cikin Malaman makarantun sakandari a jihar Kaduna ya duri ruwa

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa daga cikin mutane goma sha takwas da yan bindigan suka yi garkuwa da su sun hada da shugabar yan Yuniyon na garin, Audu Kano da sauran yayan kungiyar su bakwai.

Kwamishinan Yansandan jihar, Austin Iwar ya tabbatar da kisan jami’an Yansandan guda biyu, haka zalika wani mazaunin kauyen ya shaida ma majiyarmu cewa yan bindigan sun kai farmakin ne dauke da muggan makamai, inda suka tare hanyar da ta nufi jihar Katsina da Zamfara.

Wannan hari ya faru ne kimanin sati biyu da suka gabata, inda yan bindiga suka kashe Sojoji guda goma sha daya dake jibge a wani kauyen karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng