Kasashen Turai sun goyawa Amurka baya don kai farmaki kasar Siriya

Kasashen Turai sun goyawa Amurka baya don kai farmaki kasar Siriya

- Bayan ikirarin da shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi na cewar zai kai hari na makami mai linzami zuwa kasar Siriya saboda ya maida martani da amfani da suka yi da makami mai guba. A dai dai lokacin ne shima shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da cewar suna da gamsassun hujjoji akan amfani da makaman a kasar ta Siriya

Kasashen Turai sun goyawa Amurka baya don kai farmaki kasar Siriya
Kasashen Turai sun goyawa Amurka baya don kai farmaki kasar Siriya

Bayan ikirarin da shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi na cewar zai kai hari na makami mai linzami zuwa kasar Siriya saboda ya maida martani da amfani da suka yi da makami mai guba. A dai dai lokacin ne shima shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da cewar suna da gamsassun hujjoji akan amfani da makaman a kasar ta Siriya.

DUBA WANNAN: Trump zai fara hukunta masu amfani da shafin yanar gizo suna safarar mata

A jawabin da shugaban kasar Amurkan Donald Trump ya fitar ya bayyana cewar kasar ta Amurka tana iya mayar da martani a kowane lokaci daga yanzu.

Sai dai kuma a daya bangaren kasar Rasha tayi alkawarin harbo duk wani makami mai linzami da ake shirin harbawa zuwa Siriya.

Har ila yau shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a wata hira da yayi da manema labarai yace kasar ta Faransa tana da hujjoji masu kyau da suke nuna cewar anyi amfani da makamai masu guba a kasar Siriya.

Ita kuma Firaiministar Ingila Theresa May tana shirin gabatar da taron gaggawa a majalisar zartarwa ta kasar, saboda rade-radin cewa an kasa sanin matsaya a kasar akan shirin da kasar Amurka ke yi na kai farmaki kasar Siriya da makami mai linzami.

A wani bangaren kuwa shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel tace abisa dukkan alamu Siriya bata lalata makamanta masu guba ba kamar yadda ta fada a baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel