An samu gawar jaririn wata takwas a cikin robar ajiye ruwa bayan an rasa shi na kwana guda
Mazauna layin Obakhavbaye a birnin Benin dake jihar Edo sun shiga halin dimuwa bayan gano gawar wani jariri mai watanni takwas.
An gano gawar jaririn, Abdulaziz Abubakar Aji, a cikin wata babbar roba ta tara ruwa a dakin mahaifinsa bayan an neme shi an rasa tun ranar laraba.
Rahotanni sun bayyana cewar Abdulaziz shine yaro na biyu da iyayensa suka haifa kuma an neme an rasa tun ranar Laraba da misalin karfe 6:00 na safe.
Makwabta da abokan arzikin iyayen jaririn sun yi iya duba da cigiya domin gano jaririn amma a banza.
Saidai wasu jama'a na alakanta mutuwar yaron da sabuwar amaryar da uban jaririn ya auro a satin da ya gabata.
DUBA WANNAN: An haifi wani jariri bayan mutuwar iyayen sa da shekaru hudu
Wata majiya ta sanar da manema labarai cewar mahaifiyar jaririn ta shiga bandaki ne da safe amma koda ta fito sai ta samu jaririn baya wurin da ta barshi kwance.
Mahaifin yaron ya ki cewa komai ga manema labarai dangane da abinda ya faru.
Rahotanni sun tabbatar wa majiyar mu cewar jami'an 'yan sanda daga ofishin Aideyan sun kama mahaifin jaririn da sabuwar amaryar sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng