An sake kashe mutane 10 a wata sabuwar hari a jihar Benuwe

An sake kashe mutane 10 a wata sabuwar hari a jihar Benuwe

- Wasu da ake tsamanin makiyaya ne sun sake kai hari a wasu garuruwa biyu a jihar Benuwe

- Harin yayi sanadiyar rasa rayyuka 10 da kuma asarar gidaje da wasu dukiyoyi da dama

- Kwamishinan Yan sanda na jihar, Fatai Owoseni ya tabbatar da afkuwar lamarin inda yace jami'an sun isa garuruwan don tabattar da tsaro

Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton makiyaya ne sun kashe a kalla mutane 10 a wasu garuruwa guda biyu a jihar Benuwe. Garuruwan dai sune Gbeji da ke karamar hukumar Ukum da kuma garin Tswarev na karamar hukumar Logo.

An kuma sake kashe mutane 10 a wata hari a jihar Benuwe
An kuma sake kashe mutane 10 a wata hari a jihar Benuwe

Kwamishinan hukuma Yan sanda na jihar, Fatai Oweseni ya tabbatar da afkuwar harin a daren ranar Talata inda ya kara da cewa an gano wasu gawawaki kuma hukumar ta aike da jami'an ta zuwa garuruwan don tabbatar da tsaro.

DUBA WANNAN: Za'a bayyanawa al'umma kasafin kudin Majalisa na 2018

"An kai hari a garin Gbeji wanda muke gudanar da bincike akai. Wasu na dangata harin da makiyaya amma abin da muka tabbatar a yanzu(safiyar Laraba) shine mun gano gawawaki guda hudu a garin. Mun kara tsaurara matakan tsaro a yayin da zamu cigaba da gudanar da bincike," inji shi.

Wadanda abin ya faru a idanunsu sunce wadanda suka kawo harin sun kone gidaje da dama kuma mutane da yawa sun jikkata a harin da aka dauki sa'o'i.

Shugaban karamar hukumar Logo, Richard Nyajo, yayi kira ga hukumomin tsaro su kara dagewa wajen kare lafiya da dukiyoyin al'umma.

Babban sakataren kungiyar direbobin Najeriya (NURTW) reshen jihar ta Benuwe, Bogal Abuul wanda dan asalin garin Ukum ne yace wadanda suka kawo harin su shigo garin da muggan makamai. Abuul yace duk da cewa akwai jami'an tsaro a garin, masu harin sun ci karen su babu babaka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164