Majalisar Dokoki ta jihar Kano ta ci kamfanin sadarwa na GLO tarar N15m

Majalisar Dokoki ta jihar Kano ta ci kamfanin sadarwa na GLO tarar N15m

Mun samu rahoto da sanadin shafin jaridar Daily Trust cewa, majalisar dokoki ta jihar Kano ta nuna rashin sani da kuma rashin sabo kan katafaren kamfanin Sadarwa na Globacom, inda ta ci tarar sa N15m sakamakon gazawar sa na biyan ta harajin N47m.

Shugaban kwamitin haraji na kamfanonin sadarwa a majalisar, Alhaji Bello Butu-Butu, shine ya bayyana hakan yayin bayar da rahoton sa ga majalisar a zaman ta da ta gudanar na ranar Larabar da ta gabata.

Butu-Butu ya bayyana cewa, binciken kwamitin sa ya tabbatar da cewa kamfanin sadarwa na Globacom yana fama da kantar bashin biyan gwamnatin Kano harajin Naira miliyan 47.

Majalisar Dokoki ta jihar Kano ta ci kamfanin sadarwa na GLO tarar N15m

Majalisar Dokoki ta jihar Kano ta ci kamfanin sadarwa na GLO tarar N15m

Yake cewa, kamfanin bai biya gwamnatin Kano harajin ta ba har na tsawon shekaru uku da suka gabata.

A kalamansa, "cikin bincike da muka gudanar mun gano cewa kamafanin Globacom yana da tashoshi hasumiyar sadarwa 145 a fadin jihar sabanin 175 da gwamnatin jihar ke ikirari."

KARANTA KUMA: Mafi dadewa a kujerar Sanata ya samu karamcin majalisar Dattawa

Sai dai Butu-Butu ya bayyana cewa, kwamitin ya nemi gwamnatin jihar cikin rubutacciyar wasika da ta saukaka nauyin harajin dake kan kamfanin domin samun damar sauke shi cikin gaggawa.

Majalisar ta amince da wannan bincike inda ta kirayi gwamnatin jihar akan ta dauki tsauraran matakai kan ma su kauracewa biyan haraji a jihar.

Ta kuma kirayi gwamnatin jihar akan ta umarci dukkanin ma'aikatun samar da haraji na jihar da cewar su kara zage damtsen su wajen sauke nauyin da rataya a wuyansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel