'Danyen man da ake hakowa a Najeriya kowace rana ya ragu da ganga 82, 000

'Danyen man da ake hakowa a Najeriya kowace rana ya ragu da ganga 82, 000

- Man fetur din da Najeriya ke hakowa a duk rana ya ragu sosai

- A farkon shekara ana hako abin da ya haura ganga miliyan 2.1

- Amma yanzu ba a samun abin da ya wuce ganguna miliyan 2.02

Danyen man da Najeriya ta ke hakowa a kowace rana ta Allah ya ragu matuka a cikin ‘yan kwanakin nan kamar yadda wani rahoto daga Jaridar The Cable ta kasar nan ya nuna mana. Hakan na nufin kudin shigan Najeriya zai ragu.

'Danyen man da ake hakowa a Najeriya kowace rana ya ragu da ganga 82, 000

Abin da Najeriya ta ke hakowa na danyen man fetur ya ragu da kimanin ganga 80, 000. A watannin baya dai Najeriya na hako ganga Miliyan 2,105,656 a kowace rana. Yanzu kuwa abin da ake samu a rana bai wuce ganga 2,022,716 ba.

KU KARANTA: El-Rufai ya sa cikin Malaman Kaduna ya duri ruwa

Ma’aikatar man fetur na kasar ta bayyana wannan ko da yake dai ba a bayyana mana dalilin da ya sa man da ake hakowan ya rage yawa ba. Asali dai dama hare-haren da ake kai wa a bututun man kasar ke hana a iya hakowa mai da yawa.

A shekarar 2016 lokacin da Najeriya ta shiga cikin matsin tattalin arziki bayan tsagerun Neja-Delta sun fitini bututun man kasar sai da aka koma hako ganga miliyan 1.4 a rana. Da fetur ne dai Najeriya ta dogara wajen samun kudin shiga.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng