Jami’an Yansanda sun kwato damin makamai daga wajen yaran Buharin Daji, sun kama 11

Jami’an Yansanda sun kwato damin makamai daga wajen yaran Buharin Daji, sun kama 11

Rundunar Yansandan jihar Zamfara ta cafke wasu yan bindiga su 11, da ake zargin yaran Buharin Daji ne da suka addabi al’ummar jihar, tare da kwato damin makamai daga hannunsu.

Daily Trust ta ruwaito Kwamishinan Yansandan jihar, Kenneth Embrimson ne ya sanar da haka a ranar Laraba 11 ga watan Afrilu a garin Gusau, inda yace sun kwato bindigu guda 31 daga wajen yan bindigar.

KU KARANTA: Gimbiya sarautar mata: Manyan mata guda 10 da suka nuna bajinta a fannoni daban daban a Najeriya

Tun bayan hallaka Buharin Daji da wani tsohon Yarinsa Dogo Gide yayi ne, yaran Buharin suka fantsama kauyukan jihohin Zamfara da na Kaduna suna cin karensu babu babbaka ta hanyar yi ma mutane dayawa kisan gilla, ciki har da wasu Sojoji 11 a karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kwamishina Kenneth ya cigaba da cewa zasu gurfanar da yan bindigan gaban Kotu don fuskantar hukunci bisa laifukan da suka dinga tafkawa a jihar.

Haka zalika, Kwamishinan ya bayyana cewa sun kama yan sara suka guda 10 da suka yi kaurin suna wajen janyo tarzoma a garin Gusau, tare da wasu masu garkuwa da mutane su 2, bayan sun aika da wasikar barazana zuwa wasu kauyukan jihar.

Daga karshe Kwamishinan yace zasu cigaba da tabbatar da tsaro a yankunan jihar, don haka ya bukaci jama’an jihar da su basu goyon baya da hadin kai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel