Wani Minista ya bukaci a fara kiran Sallah da Whatsapp a Ghana

Wani Minista ya bukaci a fara kiran Sallah da Whatsapp a Ghana

- Al'ummar Musulmi na kasar Ghana sunyi fatali da wata shawara da wani Farfesa ya bayar ta cewa ladanai su koma yin kiran sallah ta manhajar sadarwar nan ta zamani wato Whatsapp, inda su kuma al'ummar musulman kasar suka nuna cewar hakan abu ne wanda ba zai taba faruwa ba a kasar domin kuwa hakan ya sabawa yanda addinin musulunci ya koyar

-An jima dai ana samun maganganu na batanci da suke nuna kyama ga addinin musulunci da mabiyansa, sai dai hakan anfi samun shi a nahiyar turai, musamman ma yankin Faransa da Italy. To sai dai abin mamaki abin ya fara shigowa Afrika inda al'ummar musulmai suke da dinbin yawa

Wani Minista ya bukaci a fara kiran Sallah da Whatsapp a Ghana
Wani Minista ya bukaci a fara kiran Sallah da Whatsapp a Ghana

Al'ummar Musulmi na kasar Ghana sunyi fatali da wata shawara da wani Farfesa ya bayar ta cewa ladanai su koma yin kiran sallah ta manhajar sadarwar nan ta zamani wato Whatsapp, inda su kuma al'ummar musulman kasar suka nuna cewar hakan abu ne wanda ba zai taba faruwa ba a kasar domin kuwa hakan ya sabawa yanda addinin musulunci ya koyar

DUBA WANNAN: Farfesan da ake zargi da neman kwanciya da dalibar sa ya gudu

Martanin al'ummar musulman kasar ya biyo bayan wata shawara da Ministan Muhalli, da Kimiyya da Fasaha, Farfesa Frimpong Boateng, yayi na cewar ya kamata ladanan kasar su daina amfani da abin sautin magana wato lasifika wajen yin kiran sallah, su koma amfani da tura sakonni ta waya ko kuma su dinga yin kiran sallar ta Whatsapp.

Boateng yace; "Mai yasa idan lokacin kiran sallah yayi baza a iya sanar da mutane ta waya cewar lokacin sallah yayi ba ko kuma ta manhajar sadarwar zamani Whatsapp?"

Sai dai kuma mai magana da yawun babban limamin kasar, a wata tattaunawa da yayi da manema labarai ya ce al'ummar musulmin kasar sunyi watsi da kiran, inda yace kiran sallah a musulunci addini ne, wanda annabi ya koyar da ayi, saboda haka babu abinda zai saka a daina yi shi ko kuma a canja yanda ake yin sa.

An jima dai ana samun maganganu na batanci da suke nuna kyama ga addinin musulunci da mabiyansa, sai dai hakan anfi samun shi a nahiyar turai, musamman ma yankin Faransa da Italy. To sai dai abin mamaki abin ya fara shigowa Afrika inda al'ummar musulmai suke da dinbin yawa, inda mutane da yawa suke ganin nuna kyamar ba zai haifarda da mai ido ba a yankin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng