Farfesan da ake zargi da neman kwanciya da dalibar sa ya gudu

Farfesan da ake zargi da neman kwanciya da dalibar sa ya gudu

- Farfesa Richard Akindele, malami ne a jami'ar Obafemi Awolowo, a garin Ile Ife dake jihar Osun, wanda ake zargi da shiryawa da wata dalibar shi a waya akan zai kwanta da ita sau biyar kafin ya bari ta tsallake jarrabawar shi

Farfesan da ake zargi da neman kwanciya da dalibar sa ya gudu
Farfesan da ake zargi da neman kwanciya da dalibar sa ya gudu

Farfesa Richard Akindele, malami ne a jami'ar Obafemi Awolowo, a garin Ile Ife dake jihar Osun, wanda ake zargi da shiryawa da wata dalibar shi a waya akan zai kwanta da ita sau biyar kafin ya bari ta tsallake jarrabawar shi.

DUBA WANNAN: Sabbin bayanai daga hukumar kidaya: Yawan 'yan Najeriya ya kai mutum 200,000,000

Idan ba a manta ba a cikin satin nan ne majiyar mu Legit.ng ta kawo muku rahoton yanda dalibar ta yada rikodin din wayar da suka yi da farfesan, wanda yake nuna muraran abinda yake bukata da ita.

Farfesa Richard, wanda yake babban Fasto ne a cocin Anglican ya jima da goge shafin sa na Facebook. Sannan kuma anyi ta faman kokarin a same shi a waya amma abin ya ci tura.

Wasu mambobi na cocin Anglican Diocese a garin Ife, dake jihar Osun sun tabbatar wa da manema labarai cewar muryar farfesan ce. Bayan haka kuma bincike ya tabbatar da cewar dalibar da yake wayar da ita tana zangon karshe ne a jami'ar, wacce ta fadi jarrabawar shi a zangon da ya wuce.

Har ila yau, farfesan wanda ake ta nema ruwa a jallo har yau bai fito ya kare kanshi ba, inda tun bayan lokacin da aka saki rikodin din ba a sake jin duriyar shi a makarantar ba.

Majiyar mu Legit.ng ta rawaito cewar hukumar makarantar ta ce tana nan tana kwakkwaran bincike akan lamarin, sannan kuma ta tabbatar da cewar zata dauki matakin da ya dace idan har ta kama wanda ake zargin da laifi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel