Gimbiya sarautar mata: Manyan mata guda 10 da suka nuna bajinta a fannoni daban daban a Najeriya

Gimbiya sarautar mata: Manyan mata guda 10 da suka nuna bajinta a fannoni daban daban a Najeriya

Duk da irin rikon sakainar kashi da al’umma da dama ke yi ma ilimin mata, Allah ya azurta Najeriya da jajirtattun mata da suka shahara a fannonin rayuwa daban daban, tare da kawo cigaba ga kasar gabaki daya, Daily Trust ta kawo guda goma.

Aloma Mariam Mukhtar: Mai shari’a Aloma Mukhtar ce mace ta farko da ta fara zama Alkalin Alkalan Najeriya, a shekarar 2013, bugu da kari itace lauya mace ta farko da ta fito daga yankin Arewacin Najeriya. Haka zalika itace mace ta farko da ta fara zama Alkali a Kotun daukaka kara, da Kotun koli.

Gimbiya sarautar mata: Manyan mata guda 10 da suka nuna bajinta a fannoni daban daban a Najeriya
Aloma

Hajara Bashir Umar: Kyawun da ya gaji Ubansa, wannan shi ne abinda Hajar ta yi, inda ta bi sawun mahaifinta, wanda ya kasance tsohon Soja ne, wanda hakan ya sanya ta shiga aikin Soja, itace mace ta farko daga yankin Arewa da ta fara kaiwa mukamin ‘Wing Commander’ a rundunar Sojan sama.

Gimbiya sarautar mata: Manyan mata guda 10 da suka nuna bajinta a fannoni daban daban a Najeriya
Hajara

Jamila Malafa: Itama Malama Jamila, zakakura ce a aikin Soja, inda ta ciri tuta a tsakanin hafsoshin rundunar mayakan Sojan ruwa, da har ta kai ta kai mukamin Commodore a rundunar, da wannan ta zamo mace ta farko yar Arewa da ta fara kaiwa ga mukamin Janar a gidan Soja.

Gimbiya sarautar mata: Manyan mata guda 10 da suka nuna bajinta a fannoni daban daban a Najeriya
Jamila

Agbani Darego: wai kowa da kiwon da ya karbe shi, inji Bahaushe, ita kuwa Darego ba Soja bace, sha’awarta shi ne harkar tallata kyawun mace, wanda hakan ya kai ta ga shiga gasar sarauniyar kyau ta Duniya, inda ta lashe kambun sarauniyar kyau ta Duniya a shekarar 2001.

Zainab Alkali: Fitacciyar marubuciya ce Hajiya Zainab, kuma kwararriyar Malama a jami’ar jihar Nassarawa, inda har ta taba shugabantar tsangayar ilimin ‘Art’, haka zalika ta rubuta kagaggun labaru da dama, da baitocin wake wake. Ana yi mata kirari da marubuciya ta farko daga Arewa da tafi shahara.

Gimbiya sarautar mata: Manyan mata guda 10 da suka nuna bajinta a fannoni daban daban a Najeriya
Zainab

Admiral Itonu Hotonu: Itonu ce mace ta farko a Najeriya da ta fara kaiwa ga mukamin ‘Admiral’ a rundunar Sojan sama, kuma an bayyanata a matsayin mace mai ilimi, basira, fikira, dabara, hazaka, aiki tukuru da sanin ya kamata.

KU KARANTA: Masana Ilimin Kimiyya sun gano kasar Sifaniya na girgiza a duk lokacin da Messi ya ci Kwallo

Chinyere Kalu: Chinyere ce mace ta farko da ta fara zama direbar jirgin sama a Najeriya, wanda kwarewarta da gogewarta a harkar sufuri ya sanya ta zama shugaban kwalejin horas da direbobin jirgin sama a Najeriya dake Zaria a shekarar 2011-2014.

Grace Alele Williams: Malama Grace ta shahara kwarai da gaske a tsakanin kwararru a fagen ilimi a Najeriya, musamman ilimin Lissafi, inda har ta kai matakin Farfesa a cikinsa, kuma ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko da ta fara zama shugaban wata jami’a a Najeriya.

Chioma Ajunwa: ita kuwa wannan matar, ta ciri tuta ne a fagen wasanni da tsalle tsalle, inda ta zamo mace ta farko a nahiyar Afirka gaba daya da ta fara lashe kyautar zinari a wasan dogon tsalle da ake yin a gasar Olympic.

Anike Agbaje-Williams: Anike ta fara aiki a gidan talabijin na yammacin Najeriya, inda ta zamto mace ta farko a Najeriya da ma Afirka kwata data fara karanta labaru a gidan talabijin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel