Tun da kun kashe min yaro, sai ku bani gawarsa – Wani Uba yana yi ma Sojoji magiya

Tun da kun kashe min yaro, sai ku bani gawarsa – Wani Uba yana yi ma Sojoji magiya

Mahaifin yaron nan mai suna Solomon Ukpe, wanda wani jami’in Soja ya kashe shi a Kaduna, Mista Andy Ita Ukpe ya bukaci rundunar Soji ta bashi gawar dan nasa, inji rahoton Daily Trust.

Tun a watan Yunin shekarar 2017 ne dai wani Soja dake aiki da makarantar sakandarin yaran Sojoji, Command ta jihar Kaduna ya kashe matashi Solomon a daidai kan mahadar titin Command, kuma har zuwa yanzu hukumar Soji ta ki mika gawarsa ga Iyayensa don su binne shi.

KU KARANTA: Yaran El-Rufai ne – Inji wasu Yan fashi yayin da suka tare sabbin Malamai 15 da Gwamnati ta dauka

Rahotanni sun bayyana cewar Sojan mai suna Ocheme Abel ya dirka ma Solomon harsashi ne a lokacin da ya aikin leburanci a wani kamfanin hada bulo, inda yake kwasar yashi daga gaban makarantar Command zuwa gidan bulon.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mahaifin mamacin, Andy Ukpe yana shaida ma yan jaridu cewar yana bukatar Sojoji su bashi gawar dansa, tare da diyyar kudi naira miliyan 700 don ya kula da yara guda biyu da dan nasa ya bari.

Mahaifin ya kara bayyana yadda aka kashe masa da, inda yace: “Yarona lebura ne, kuma kafinta ne, a ranar da ak kashe shi ya tafi debo yashi ne a gaban Command zuwa don hada bulo, sai Sojan ya umarce shi da ya daina diban yashin, shi kuma yayi masa bayanin aikin da yake yi.

“Daga nan sai Sojan yayi kamar ya fahimci maganarsa, sai ya aike shi ya siyo masa sigari, juyawarsa ke da wuya da nufin siyo masa sigarin, sai ya dirka masa harsashi ta baya, nan take ya fadi matacce. Bayan nan Yansanda sun garzaya da gawar zuwa Asibitin gwamna Awan, amma daga bisani Sojoji sun dauke gawar.” Inji shi.

Daga karshe yace bayan shigar da kara ga hukumar kare hakkin dan Adam, Sojojin sun bashi damar ganin gawar dansa, kuma yace ya aika da wasiku zuwa ga babban hafsan Sojan kasa, amma bai samu wani martani daga gareshi ba, don haka ya dauki alwashin zai shigar da kara Kotu idan aka cigaba a haka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel