Ku rage tsadar magani da ganin likita - Haj. Aisha Buhari ga asibibitoci da ba na gwamnati ba

Ku rage tsadar magani da ganin likita - Haj. Aisha Buhari ga asibibitoci da ba na gwamnati ba

- Matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta bukaci cibiyoyin kiwon lafiya na kudi a Najeriya da su rangwanta kudin da suke karba don aikin su a kasar

- Matar shugaban tayi Kiran ne a lokacin da kungiyar likitocin gwamnati da masu zaman kansu ta Najeriya suka kai mata ziyara a ranar laraba a ofishin ta dake gidan gwamnati a Abuja

Ku rage tsadar magani da ganin likita - Haj. Aisha Buhari ga asibibitoci da ba na gwamnati ba
Ku rage tsadar magani da ganin likita - Haj. Aisha Buhari ga asibibitoci da ba na gwamnati ba

Ta lura da cewa mafi yawan yan'najeriya da basu da damar zuwa cibiyoyin lafiya na Gwamnati na karewa ne a cibiyoyin lafiya masu zaman kansu wadanda suke da tsada. Wanda sakamakon ba akan mara lafiyan kadai yake tsayawa ba, harda kasar baki daya.

Tace "Cibiyar lafiya ta kudi tana da tsada, kungiyar ku yakamata ta kara duba yanda kuke karbar kudin"

A maganar da Sulaiman Haruna, shugaban yada labarai na ofishin matar shugaban kasar yayi, yace matar shugaban kasan tana koken yanda sashin lafiya ya zama, tace mutane suna fita kasashen waje ne so da yawa likitocin najeriya suke tararwa.

Tace "Ina kira ga kungiyarku da su duba abubuwan da basu dace ba dake faruwa a asibitocin kudi wadanda basu dace ba.

Ta jawo hankalinsu da suyi hadin guiwa tsakanin asibitocin Gwamnatin da na kudi ta yanda na kudin zasu iya zuba hannun jari a bangaren lafiyan domin su ragewa Gwamnatin nauyi. "shiyasa nake shirin hada taron wadanda abun ya shafa, domin jawo hankalinsu"

Shugaban kungiyar Dr. Frank Odofen, yayi jinjina ga matar shugaban kasar ta yanda take maida hankali akan lafiyar mata da kananan yara a kasar wanda sakamakon haka ne aka zabeta a matsayin jakadiyar UNAIDS, saboda tabbatarwa da akayi da cewa cibiyoyin kiwon lafiya zasu samu cigaba a Najeriya.

DUBA WANNAN: Yawan yan Najeriya a bana

Shugaban kungiyar likitocin iyali na duniya, farfesa Amanda Howe, wanda ya kawo ziyarar kwanaki biyu a Najeriya, ya lura da furuci da kuma shirye shiryen uwargidan shugaban kasar sun cancanci ayi koyi dasu.

Tace, ma'aikatan lafiya da ke aiki a Najeriya suna aiki tukuru tare da goyon baya da kuma gujewa cutuka ta hanyar wayar da kai ga iyali da marasa lafiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel