Gasar zakarun Turai: Messi ya zargi kungiyar Manchester United a kan rashin nasarar kungiyar Barcelona a hannun Roma

Gasar zakarun Turai: Messi ya zargi kungiyar Manchester United a kan rashin nasarar kungiyar Barcelona a hannun Roma

Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi, ya zargi sha'awar da kungiyar Manchester United ta nuna a kan dan wasan su na baya, Samuel Umtiti, da zama silar rashin nasarar kungiyar a wasan da ta buga da kungiyar AS Roma a gasar cin kofin zakaru na nahiyar Turai.

Wata jaridar wasanni a kasar Sifen ta rawaito cewar Messi ya yiwa Umtiti fada har saida bakinsa ya yi kumfa yayin da aka tafi hutun rabin lokaci a wasan. Jaridar ta ce, Messi ya zargi Umtiti da kin mayar da hankali a kan wasan saboda tunanin tayin da Manchester United suka yi masa.

Messi ya zargi kungiyar Manchester United a kan rashin nasarar kungiyar Barcelona a hannun Roma
Messi

Kungiyar Manchester United ta nuna sha'awar daukan, Umtiti, dan wasa bayan na Barcelona, a karshen kakar wasanni ta bana.

DUBA WANNAN: Kotun Najeriya ta saki wasu mayakan kungiyar Boko Haram, ta dora laifin kan gwamnatin tarayya

A nasa bangaren, Umtiti ya bukaci kungiyar Barcelona tayi masa karin albashi ko kuma ya hada kayansa ya koma kungiyar Manchester United da taka leda.

Kazalika mai Kulob din Barcelona ya zargi tsohon kociyan Manchester United, Sir Alex Ferguson, da taimakawa kungiyar Roma da dabarun wasa da suka basu nasara a kan Barcelona. Yayin wasan, an hangi Sir Alex zaune a layin dake bayan mai kulob din Roma a sashen manyan baki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng