An kashe wani dan kasuwar kasar Syria a Kano

An kashe wani dan kasuwar kasar Syria a Kano

Wasu masu garkuwa da mutane da ba'a san ko su wanene sun kashe wani dan kasuwa, dan asalin kasar Syria, Ahmed Abu Areeda kuma suka sace dansa Muhammad Ahmed mai shekaru 14 a jihar Kano.

Masu garkuwa da mutanen sun harbe dan kasuwan ne a ranar Talata bayan yaki amincewa su sace dansa kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne misalin karfe 8.05 na dare yayin da mamacin tare da yaransa biyu suka tafi ofishin Kungiyar taimakon gagawa na Red Cross a garin Kano don ya dauke motar sa.

An kashe wani dan kasuwar kasar Syria a Kano
An kashe wani dan kasuwar kasar Syria a Kano

Wasu wanda abin ya faru a idanunsu sunce yan bindigar su takwas ne suka far wa mamacin da yaransa yayin da yaje daukar motar sa a harabar ofishin kungiyar Red Cross.

DUBA WANNAN: Dubi sunayen 'Yan sandan da suka garkame wani a bandakin banki saboda yaki basu cin hanci

Wani ganau daya bukaci a sakaya sunnansa yace, "Ya rufe shagon sa misalin karfe 8.00 na dare inda ta kama hanya zuwa harabar kungiyar Red Cross daya saba ajiye motarsa. Kwatsam sai yan bindigar da suka ajiye motarsu kirar Peugeot mai launin kore da suke jiran shi suka biyo shi cikin harbar kungiyar yayinda wasu suka tsaya a mota.

"Wadanda suka biyo shi cikin harabar Kungiyar ta Red Cross sun harbe shi a kai sannan suka dauke dansa guda daya mai suna Muhammad."

Wani wanda suke aiki tare da mamacin shima daya bukaci a sakayya sunansa ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa mamacin ya shafe shekaru 20 yana zaune a Najeriya. Yayi aiki ne a matsayin Akanta da 'Nigerian Braiding Manufacturers' (NBM) na tsawon shekaru 10 kafin daga bisani ya bude kasuwancin nasa.

Kakakin hukumar Yan sanda SP Magaji Musa Majia ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace ana kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne suka zo sace yaron kuma suka kashe mahaifin. Majia ya kara da cewa hukumar ta fara bincike akan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel