Dubi sunayen 'Yan sandan da suka garkame wani a bandakin banki saboda yaki basu cin hanci

Dubi sunayen 'Yan sandan da suka garkame wani a bandakin banki saboda yaki basu cin hanci

- Hukumar Yan sanda ta gano jami'an da suka kulle wani mutum a bandakin wata banki saboda yaki basu cin hanci

- Mutumin marubuci ne mai suna Ibe-Anyawu yace sunce masa shi dan damfara ne kuma suka bukaci ya basu kudi

- Hukumar Yan sandan ta binciko su kuma suna amsa tambayoyi kafin a dauki matakin hukunci akansu

Hukumar Yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta bayyana sunayen jami'an sandan yaki da fashi da makami (SARS) wandanda rannan Litinin suka gurkame wani marubuci mazaunin Legas, Immanuel Ibe-Anyawu a bandakin banki na tsawon sa'o'i.

Ibe-Anyawu ya labarta yadda jami'an Yan sandan suka ci mutuncinsa inda sukayi ikirarin cewa she dan damfara ne kuma suka bukaci ya basu cin hanci.

An sanar da sunayen 'Yan sandan da suka kulle wani marrubuci cikin ban daki a Legas
An sanar da sunayen 'Yan sandan da suka kulle wani marrubuci cikin ban daki a Legas

A sanarwan da hukumar ta fitar ranar Laraba, ta bayyana cewa ana gudanar da bincike akan jami'an guda biyar wanda suke aiki da sashin yaki da masu fashi da makami na Ipakodo ba Ikeja ba kamar yadda aka ambata da farko.

DUBA WANNAN: Mutan garinsu Ben-Bruce sun fara juyawa salon siyasar sa baya

Sunayen 'yan sandan sun hada da Inspector Taiwo Omojope, Inspector Arigidi Ebibor, da kuma Saja Rotimi Adesoba, Olalekan Olakunle da kuma Friday Oni.

A halin yanzu, ana musu tambayoyi a ofishin hukumar kafin daga bisani a mika su zuwa ga sashin hukunta masu laifi don ayi musu shari'a.

Sanarwan kuma ta kara da cewa akwai wani jami'i mai suna Jude Akhoyemta wanda daga farka aka ambaci sunansa cikin yan sandan da suka tsare mutumin amma daga bisani bincike ya wanke shi.

A ranar Talata, Ibe-Anyawu ya shaida wa Cable news cewa hukumar Yan sandan sun gayyace shi don yazo ya nuna jami'an da suka ci zarafinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel