Kungiyar AS Roma tayi waje da Barcelona yayin da Liverpool ta yi kaca-kaca da City

Kungiyar AS Roma tayi waje da Barcelona yayin da Liverpool ta yi kaca-kaca da City

- AS Roma ta ba Duniya mamaki bayan tayi waje da Barcelona jiya

- Barcelona da ta ci 4-1 a wasan farko ta yi waje bayan an ci ta 3-0

- Liverpool kuma ta kara lallasa Man City da ci har 5-1 gida da waje

Yanzu haka dai Kungiyar AS Roma da Liverpool sun ba Duniyar kwallo mamaki bayan da su ka yi waje da Kungiyar Barceclona da kuma Manchester City daga Gasar Zakarun Nahiyar Turai.

Liverpool da Roma sun kafa tarihi a kan Manchester City da Barcelona
Liverpool da Roma sun kafa tarihi a wasan daren jiya

Barcelona ta gamu da abin da ya rikitawa magoya bayan ta tunani bayan da aka yi waje da ita daga Gasar Champions league na Turai a daren jiya da ci 3-0 bayan a wasan farko ta lallasa Kungiyar AS Roma da ci 4-1.

KU KARANTA: Abubuwa 7 da za su iya sa Shugaba Buhari ya sha kasa

Haka za-lika kuma Kungiyar Pep Guardiola ya kuma shan kashi a hannun Liverpool wani karon da ci 2-1 har gida. Duk da Man City ta fito da niyyar bada mamaki sai ma dai ya zama kunya ta kara sha a gidan ta a daren jiya.

Liverpool ta samu zuwa wasa na-kusa da karshe a Gasar Zakarun Nahiyar Turai karo na farko cikin shekara 10 yayin da AS Roma ta samu isa zagayen karo na farko a tarihin Kungiyar. A wasan fari dai an ci City 3-0.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng