Gwamnatin jihar Kadun ta kama yan ‘Sara Suka’ 70 dake fitinan jama’an Kaduna
Akalla yan ‘Sara Suka’ guda 70 ne da suka addabi al’ummar jihar Kaduna ne jami’an Yansandan jihar suka kama, kamar yadda Kwamishinan Yansandan jihar, Austin iwar ya bayyana.
Legit.ng ta ruwaito Kwamishinan yana cewa sun kama makamai da suka hada da adduna, gorori, da gariyo da dama daga hannun yan Sara sukan, haka zalika yace yan daban na basu muhimman bayanai a binciken da suke gudanarwa.
KU KARANTA IBB ba Allah bane, Obasanjo ba Allah bane, babu yadda zasu yi da Buhari – Ministan Buhari
Idan za’a tuna a kwanakin baya ne wasu yan shara suka kaddamar da hare hare a unguwannin Kawo, Badarawa da Kwaru, inda har suka datse ma wani mutumi, tsohon Soja, da bai ji ba, bai gani ba, hannu.
A wani hari na ramuwar gayya da wasu matasa yan sara suka na daban suka kaddamar, sun kone gidage guda uku kurmus, da wani gidan Burodi, wanda hakan ya tayar da hankulan jama’an unguwannin.
A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jihar Kaduna ta sanar da kwato manyan makamai da dama daga hannun mazauna jihar Kaduna da suka hada da samfurin bindigu daban daban guda 111, da kayan tsafe tsaye guda 120, Babura guda 3, kwalekwalen Sojoji guda 3, adduna 30 da kwari da baka guda 2.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng