Wata mai kula da gidaje tayi yunkurin cizge mazakutar wani dan haya
An gurfanar da wata mai kula da gidaje, Judy Rweso a gaban kotu idan ake tuhumarta da laifin yunkurin cizge mazakutar wani dan haya a unguwar Zimmerman da ke garin Nairobi a kasar Kenya.
Ana tuhumar Rweso da cin zali da kuma yunkurin yin lahani ga mazakutar Boniface Waweru a ranar 10 ga watan Maris inda yanzu ta bar shi cikin azaba da radadi.
Rahotanni sun bayyana cewa Waweru yayi makarar farkawa daga barci kuma ya tafi bakin pampo don ya wanke bakinsa sai ita kuma Judy ta zo wucewa ta fara dirka masa ashar. Bisa ga dukkan alama tayi tsammanin shine yake kwankwasa mata kofa a daren daya gabata.
A cewar kafar yadda labarai na Kenya Pulse,daya daga cikin makwabtan wanda abin ya faru a idanunsa ya kira su taron sulhu da yamma bayan Judy ta musanta cewa ta zagi Waweru.
DUBA WANNAN: Kungiyar kwadago na kasa ta bukaci karin albashi mafi karanci a Najeriya
"A wurin taron sulhun, ran Judy ya baci sosai saboda anyi cincirindo akanta inda wai ta ci mutuncin mutumin da bai aikata laifin komai ba. Hakan yasa ta daka tsalle ta cafko mazakutar Wawero kuma ta fizge su da karfi inda yayi ta shan azaba."
Mutane sun taso za suyi wa Judy hukunci amma ta tsere shiga kuma Waweru ya shigar da kara ofishin yan sanda. Daga baya an gano inda Judy ta buya kuma aka gurfanar da ita gaban kotun Makadara da ke Nairobi.
Judy taki amsa laifin da ake tuhumarta da aikatawa inda tace an tsare da a ofishin yan sanda na tsawon kwanaki biyar a jere ba tare da an gurfanar da ita gaban kotu ba wanda ya sabawa kundin tsarin kasar.
Kotu ta bukaci dan sandan daya shigar da karar ya gurfana gaban kotu don karin haske kan lamarin kuma ta dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Afrilu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng