Bayan shekaru 13 NNPC ta ware Dala Biliyan 2.8 don aikin bututu daga Ajaokuta - Kaduna - Kano

Bayan shekaru 13 NNPC ta ware Dala Biliyan 2.8 don aikin bututu daga Ajaokuta - Kaduna - Kano

- Matatar man fetur ta kasa NNPC ta sa hannun kwangilar akan aikin gina bututun gas wanda zai tashi daga Ajaokuta, Kaduna zuwa Kano

- Idan ba a mance ba a shekarar 2008, gwamnatin tarayya ta amince da tsarin gas na Najeriya wato Nigerian Gas Master Plan, domin cigaban aikin bututun gas na gida da kasuwar waje

Bayan shekaru 13 NNPC ta ware Dala Biliyan 2.8 don aikin bututu daga Ajaokuta - Kaduna - Kano
Bayan shekaru 13 NNPC ta ware Dala Biliyan 2.8 don aikin bututu daga Ajaokuta - Kaduna - Kano

Matatar man fetur ta kasa NNPC ta sa hannun kwangilar akan aikin gina bututun gas wanda zai tashi daga Ajaokuta, Kaduna zuwa Kano.

Idan ba a mance ba a shekarar 2008, gwamnatin tarayya ta amince da tsarin gas na Najeriya wato Nigerian Gas Master Plan, domin cigaban aikin bututun gas na gida da kasuwar waje.

DUBA WANNAN: Wata daliba ta saki sakon muryar dake nuna wani Farfesa yana son kwanciya da ita kafin ta haye jarrabawar shi

Farkon aikin zai fara daga Ajaokuta zai biyo ta birnin tarayya Abuja sai jihar Kaduna sai kuma ya tsaya a jihar Kano.

Sa hannun kwangilar tsakanin matatar man fetur ta kasa da kamfanonin hadin guiwa na Chinese wanda shine na farko a tarihin Najeriya, aikin bututun gas din mai fadin inchi 40 da tsawon kilometre 614.

Kamar yanda karamin ministan man fetur, Ibe Kachikwu ya fada "kwangilar ta dau tsawon shekaru 13, hakan ya faru ne bisa samun ci baya ta dalilin rashin isasshen kudin aikin da gwamnatin tarayya tayi fama dashi.

Aikin dala biliyan 2.8 na bututun gas din na daya daga cikin zababbun aiyuka guda uku. Egina dala biliyan 15,Bonga dala biliyan 10,ana sa ran zasu jawo hannayen jari na dala biliyan 40 domin gyaran tsarin gas na Najeriya.

Cigaban da ake samu a aiyukan ma'aikatar man fetur din karkashin shugabancin Maikanti K. Baru, shugaban ya cigaba da samun jinjina daga mutane daban-daban domin kokarin da yakeyi don ganin ya kawo cigaba a kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel