'Yan bindiga cikin kakin 'yan sanda sun kashe DPO
Wasu 'yan bindiga sun harbe jami'in 'yan sanda, Mista Kingsley Chukwueggu, mai mukamin DPO dake rike da ofishin hukumar dake Rumuolumeni a jihar Ribas.
Rahotanni sun bayyana cewar 'yan bindigar da suka harbe Chukwueggu na sanye da kakin 'yan sanda sannan sun saka shingen kan hanya a titin Asa dake yankin Obiehie a jihar Abiya.
Jaridar Punch ta rawaito cewar DPO Chukwueggu ya yi bulaguro a karshen makon jiya domin ziyartar dattijuwar mahaifiyar sa dake karamar hukumar Abo Mbaise a jihar Imo.
'Yan bindigar da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, sun fara sace wasu mutane bakwai da misalin karfe 7:45 sannan suka ajiye su gefen hanya.
DUBA WANNAN: Shugabannin kasashe 7 da suka fi Bill Gates kudi da adadin abinda suka mallaka
Marigayin, ya daka tsawa ga 'yan bindigar bayan isowar sa wurin bisa tunanin jami'an 'yan sanda ne na gaske. Bayan ya fito daga motar sa ne sai suka sassare shi da adda sannan suka harbe shi.
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Ribas, Mista Nnamdi Omoni, ya tabbatar da mutuwar Chukwueggu tare da bayyana cewar tuni sun fara bincike a kan lamarin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng