Shugabannin kasashe 7 da suka fi Bill Gates kudi da adadin abinda suka mallaka

Shugabannin kasashe 7 da suka fi Bill Gates kudi da adadin abinda suka mallaka

Attajirin kasar Amurka, Bill Gates, ne jaridar Forbes ta bayyana a matsayin wanda ya fi kowa kudi a duniya da adadin Dalar Amurka biliyan $80bn.

Saidai wani binciken bin kwakwkwafi ya bayyana cewar, Bill Gates ya zama na daya ne saboda shi dan kasuwa ne, amma akwai wasu shugabannin kasashe da wasu 'yan tsirarun mutane da suka tara dukiya ta haramtacciyar hanya da suka fi na Bill Gates.

Ga jerin wasu shugabannin kasashe 7 da rahoton ya bayyana sun fi Bill Gates kudi:

7. Kim Jong- Un: Shugaban kasar Koriya ta Arewa mai ci. Duk da talaucin da kasar Koriya ta Arewa ke fama da shi, dangin shugaban kasar sun mallake dukiyar kasar.

Shugabannin kasashe 7 da suka fi Bill Gates kudi da adadin abinda suka mallaka
Kim Jong-Un

Bincike ya tabbatar da cewar, Kim Jong-Yung, ya mallaki kudin da adadinsu ya kai Dalar Amurka biliyan $170bn.

Ya mallaki gidajen alfarma, jiragen sama da kayan kawa na zinare.

6. Muammar Gaddafi: Hambararren shugaban kasar Libiya, Gaddafi, ya mallaki dumbin dukiya ta hanyar mayar da asusun kasar Libiya tamkar lalitar sa ta hanyar daukan kudi domin bukatar kansa ko ajiye su a asusun bankunan dake fadin duniya.

Shugabannin kasashe 7 da suka fi Bill Gates kudi da adadin abinda suka mallaka
Gaddafi

Bindigar Gaddafi ta zinare ta zama abar magana a tsakanin mutane da dama.

Rahotanni sun bayyana cewar Gaddafi ya mallaki Dalar Amurka $180bn kafin a guguwar juyin-juya-hali ta tafi da shi a shekarar 2011.

5. Gidan Sarautar Saudiyya: Anyi ittifakin sune dangin da suka fi mallakar dumbin kudi. Suna da matukar sirri domin basa bukatar kowa ya san takamaiman adadin abinda suka mallaka kuma hakan ya saka basa cikin jerin masu kudin Duniya na jaridar Forbes.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya musanta amincewa da kashe biliyan $1 domin sayen kayan aiki ga sojin Najeriya

Bincike ya gano cewar sun mallaki kudi da adadinsu ya kai Dalar Amurka tiriliyan $2tn zuwa tiriliyan 2.4tn.

4. Bashar Al-Assad: Shugaban kasar Syria mai fama da yaki. Yana sarrafa dukiyar kasar yadda ya ga dama.

Duk da ya bayyana cewar ya mallaki Dalar Amurka biliyan 1.50bn, bincike ya tabbatar da cewar, ya fadi hakan ne domin nuna shi ba barawo bane. Wani binciken kwakwaf ya gano cewar, Al-Assad, ya mallaki fiye da Dalar Amurka biliyan $122bn a boye a bankuna dake kasar Fanama.

3. Hosni Mubarak: Tsohon shugaban kasar Egypt da aka hambarar a juyin-juya-hali na shekarar 2011.

Mubarak ya mulki kasar Egypt daga shekarar 1981 zuwa shekarar 2011 kuma ya mallaki Dalar Amurka biliyan $70bn.

Mubarak, mai shekaru 89 a duniya, na cigaba da gudanar da rayuwa mai tsada duk da an tunkude shi daga kan mulki.

2. Ali Abdallah Saleh: Shugaban kasar Yemen na tsawon shekaru 30 kafin guguwar juyin-juya-hali ta tunbuke shi daga kujerar mulki a shekarar 2011.

Saleh ya yi fice wajen mallakar dumbin kudi da kuma yin kyautar wuce kima ga matan da yake hulda su.

Rahotanni sun bayyana cewar ya mallaki Dalar Amurka da adadinsu ya kai biliyan $126bn.

1. Vladimir Putin: Shugaban kasar Rasha kuma mutum mafi karfin iko yanzu haka, a fadin duniya.

Shugabannin kasashe 7 da suka fi Bill Gates kudi da adadin abinda suka mallaka
Vladimir Putin

Putin mutum ne da ya yi fice wajen mallakar ababen hawa na musamman, masu tsadar gaske.

Bincike ya gano cewar, Putin, na da kimanin Dalar Amurka biliyan $200bn a bankunan kasar Fanama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel