Dandalin Kannywood: Na yi da-na-sanin soyayyar da muka yi tare da Timaya - Zee Zee
Fitacciyar tsohuwar jarumar finar finan Kannywood, Ummi Zee Zee ta bayyana cewa babban kuren da ta tafka a rayuwarta kuma take dana-sanin yin hakan shi ne soyayyarta da shahararren mawaki Timaya.
Zee Zee ta bayyana haka ne cikin wata hira da tayi da jaridar Daily Nigerian, inda ta yi raddi game da wani jita jita da ake yadawa na cewa wai ta sauya zuwa addinin Kirista saboda tarayyarta da Timayan.
KU KARANTA: BTsohon shugaban kasa ya gurgfana gaban Kotu don amsa tuhume tuhumen cin hanci da rashawa
A cikin hirar, Zee Zee ta bayyana cewar tana matukar girmama marigayi dan Ibro da marigayiya Aisha Dan Kano, sa’annan tace ita mutumce mai yawan karanta Al-Qur’ani da Hadisan Manzon Allah don kara samun haske a Musulunce.
Da aka tambayeta game da shirin aure, Zee zee ta tabbatar ma majiyar Legit.ng cewar a yanzu haka ta shirya yin aure, kuma tana rokon Allah ya tabbatar mata da burinta daga yanzu zuwa karshen shekara.
Daga karshe ta tabbatar da cewar ita mai kudi ce, don haka ta daina fitowa a fina finan Kannywood, inda tace “Nawa za’a biya ni?”, ta kara da cewa tana da arziki sosai, don haka idan ma wani yayi mata kyautan wasu yan miliyoyi ba zata gode masa ba, don kuwa ta fi karfinsu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng