An kama Makiyayi dauke da manyan bindigogi a Jihar Enugu

An kama Makiyayi dauke da manyan bindigogi a Jihar Enugu

- Jami’an tsaro sun kama wani Makiyayi dauke da bingiga a Enugu

- Yanzu haka wannan Bawan Allah na tsare a hannun ‘Yan Sanda

- A kwanakin nan ana samun rikici tsakanin Makiyaya da Manoma

A kwanan nan ne mu ka ji labari daga Jaridar Daily Trust cewa an yi ram da masu barna a Jihar Enugu. Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun damke wani Makiyayi ne dauke da makamai a Garin.

An kama Makiyayi dauke da manyan bindigogi a Jihar Enugu
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun damke Makiyaya a Enugu

Kamar yadda labarin ya zo mana wani Makiyayi ya shiga hannu bayan da aka kama shi da bindigar AK-47 da kuma tarin harsashi mai mita 7.62 a Garin Isigwe Ugbawka da ke Karamar Hukumar Nkanu ta Gabas a Jihar Enugu.

KU KARANTA: An bayyana lokacin da za a samu tsaro a Yankin Boko Haram

Yanzu haka wannan Makiyayi da aka kama yana cigaba da taimakawa jami’an tsaro wajen binciken da su ke yi a kan lamarin na rikicin Makiyaya. Mai magana da bakin ‘Yan Sandan Jihar Ebere Amraizu ya fadi wannan.

Yanzu haka dai Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Enugu ya bada lambar wayoyin da za a bukata da zarar an shiga wata tarzoma. Mutanen Garin na Nkanu ta Gabas sun tabbatar da cewa babu rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel