Sunayen barayin gwamnati: Ko dai a bani hakuri, ko kuma mu hadu a kotu - Dokpesi
- Mai kamfanin sadarwa na Daar PLC, Raymond Dokpesi, yayi korafi akan sunansa da aka saka cikin sunayen barayin gwamnati
- A takardar da ya aikawa Ministan Labarai, Lai Mohammed ta hanyar lauyansa, yace bayyana sunayen da Ministan yayi bata suna ne
- Dokpesi yanzu haka yana fuskantar shari’a bisa zargin da ake masa da karbar N2.1bn daga hannun mai bawa shugaban kasa ta fannin tsaro
Mai kamfanin sadarwa na Daar PLC, Raymond Dokpesi, yayi korafi akan sunansa da aka saka cikin jerin sunayen wadanda suka saci kudaden gwamnatin tarayya kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A takardar da ya aikawa Ministan Labarai, Lai Mohammed, a ranar 4 ga watan Afirilu, 2018, ta hanyar lauyansa, Mike Ozekhome (SAN), Dokpesi yace bayyana sunayen da Ministan yayi bata suna ne.
DUBA WANNAN: An bukaci fadar shugaban kasa da sauran ma'aikata su bayyana kudaden suke kashewa wajen hidimar ofisoshinsu
Dokpesi yanzu haka yana fuskantar shari’a a birnin tarayya, bisa zargin da ake masa da karbar N2.1bn daga hannun mai bawa shugaban kasa ta fannin tsaro (NSA) tun a shekarar 2015, wanda har yanzu ake daga sauraron karar ba tare da an yanke hukunci ba.
Ozekhome yace bayyana sunayen da akayi ya lalatawa wanda nake karewa suna, “wanda ya dade yana nema kafin ya samu”, wanda hakan ya janyo masa matsaloli a kwakwalwarsa harma da asarar hanyoyin kasuwancinsa.
A wasikar da Ozekhome ya aikewa Lai Mohammed, yace muddin ba'a basu hakuri ba kuma an cire sunan wandan yake karewa daga sunayen barayin, bazasuyi wata-wata ba wajen maka shi a kotu kuma su bakashi a biya su diyya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng