Cututtuka da aka iya samu a gurbataccen ruwan-sha a karkara

Cututtuka da aka iya samu a gurbataccen ruwan-sha a karkara

- Cututtukan da ake samu daga gurbataccen ruwansha suna da yawa

- Ruwan sha dai ya zama wani kayan gabas a kasashe masu tasowa

- Anfi daukar cuta a ruwa in aka kwatanta da ta iska, ta kuma fi iya kisa

Cututtuka da aka iya samu a gurbataccen ruwan-sha a karkara
Cututtuka da aka iya samu a gurbataccen ruwan-sha a karkara

Kauyen Paikon Kore, dake wajen garin Abuja, rafin Eku shine hanyar samun ruwa da tafi kowacce ga jama'ar yankin, fulani da gwarawa, sai dai hakan na nufin muggan cututtuka da ke ruwan suna kara yaduwa cikin jama'ar yanki da gaggawa.

Ruwan Eku dai, da aka bincika, yafi kowanne ruwa hadarin kamuwa da cututtuka a yankin, inda aka sami akalla dangogin bacteriya 6,000 a lita da ta ruwan a qoqo. Dangogin ire-iren cutar kenan fa, ba wai yawan kwayoyin cutar ba.

DUBA WANNAN: Kisan GIlla a Offa na jiya: Yadda suka kitsa harin

Daga cikin irin wadannan bacteriya da ma kuma viruses da fungus, watau funfuna, wadanda suma suna kawo irin nasu cututtukan. E. Coli, bacteriya ce da take kawo da har zai kai ga zawon jini. Salmonella Typhi ke kawo taifot ta zazzabi.

Vibrio Cholerae ke kawo cutar amai da gudawa watau Kwalara. Akwai kuma wasu dabam suma, kari kuma akwai cutuka kamar kurkunu, da matsotsa masu shan jini.

A karkashin karaqmar hukumar Gwagwalada garin Paiko yake, yana kuma da jama'a akalla 10,000, wanda hakan ke nufin gwamnatin Abujar bata kula da rayuwar wadanda basu birni.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng