Jerin sunayen barayi: Uche Secondus na PDP ya kai Lai Muhammed kara, yana neman diyyar biliyan daya da rabi
Mista Mohammed ya ambaci Mista secondus a cikin jerin wadanda ake zargi da kwashe kudin kasar, wai shugaban jam'iyyar PDP ya karba Naira miliyan 200 daga tsohon mai bada shawara akan harkokin tsaro na kasa (NSA).
A yanda ya nuna ta lauyan shi, Mista Emeka Etiaba, ya musanta karbar kudin. Ya fadama ministan da ya janye sunan shi daga jerin sannan ya bashi hakuri a bayyane da kuma biyanshi Naira biliyan daya da rabi na bacin suna a cikin sa'a arba'in da takwas.
Nan da sa'a 72 daga yau daga yau(March 31,2018),zamu je kotu domin mu shigar da kara kuma mu kare hakkin shi. Lauyan Secondus ya fadama Mohammed a wasikar da yayi mishi asabar din satin da ya gabata.
A sakamakon kasa cika sharuddan da suka gindaya mishi, shugaban PDP din ya tabbatar da ba tsoratarwa kadai yayi ba, domin kuwa ya shigar da kara a fatakwal a babban kotun jihar Rivers
A karar da ya shigar mai lamba PHC/1013/2018,ya bukaci kotun da ta karbar mishi Naira biliyan daya da rabi na cin mutuncinshi da akayi, bacin suna da nagarta sakamakon buga sunanshi da akayi.
Yace wai sunayen da ministan ya fitar bacin suna ne kuma yana rokon kotun da ta umarci Mohammed da ya janye bugun da yayi kuma ya bada hakuri a rubuce.
Secondus zai so bada hakurin ya kasance a rubuce a dukkanin kafafen yada labarai inda tun da farko ya fara yadawa.
Ya kuma roki kotun da ta hana wanda yake kara sake buga makamancin cin fuska irin haka.
A kotun akwai Gwamnatin tarayyar najeriya wacce shugaban yan sanda ya wakilta da kuma kamfanin buga jarida. Duk da haka ministan har yanzu bai ce komai ba.
DUBA WANNAN: Aftawan Indiya da basu yi Boko ba
Mista Mohammed ya fada ma manema labarai ranar a juma'ar da ta gabata cewa an yanke shawarar bayyana sunayen sakamakon Kiran da PDP tayi ga Gwamnatin da ta buga sunayen wadanda suka rarumi dukiyar Najeriya.
Jerin sunayen ya hada da sakataren PDP na yada labarai, Mista Olisa Metuh da kuma mataimakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Dudafa Waripamo-Owei.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng