Sojin Amurka 12 da suka horas da sojin Najeriya sun bayar da labarin zaman su a Jaji

Sojin Amurka 12 da suka horas da sojin Najeriya sun bayar da labarin zaman su a Jaji

- Dakarun soji 12 daga kasar Amurka ne suka zon Najeriya don taimakwa sojin Najeriya da shawarwari da horo

- An zabo sojojin ne daga wasu tawaga na musamman da suka kware wajen yaki, hawa duwatsu da kuma bayar da horo kan tsaro

- Aikin su shine koyar da sojojin kasa na Najeriya dabarun yaki

Wasu sojojin kasar Amurka guda 12 da sukayi makonni shida a Najeriya suna bayar da sharwarwari da horo ga sojojin kasa na Najeriya a sansanin soji na Jaji da ke Kaduna sun bayyana irin yadda suka rayuwar da sukayi lokacin ziyarar.

Sojojin Amurkan sun bayyana wannan labarin ne a wata labari da aka wallafa a shafin yanar gizo na hukumar a ranar Laraba. Sun bayyana cewa duk abubuwan da suke tsamani ya zama gaskiya musamman yadda suka lura cewa babu ababen more rayuwa da suka saba dasu kamar na'urar sanyaya daki, yanar gizo, isashen ruwan pampo da kuma kayan kwalama kamar pizza da burger king.

Sojin Amurka 12 da suka horas da sojin Najeriya sun bayar da labarin zaman su a Jaji
Sojin Amurka 12 da suka horas da sojin Najeriya sun bayar da labarin zaman su a Jaji

"Mu da kanmu muke zuwa wata babban pampo don mu dibo ruwan da zamuyi amfani dashi a bayan daki tunda ruwan ba kowane lokaci ake samunsa ba," kamar yadda Captain Aaron Harris ya bayyana.

Harris ya cigaba da cewa basu da matsalar wajen kwana don an basu gadaje da yawa tare da gidan sauro. Ya kuma ce samun gangariyan abinci don sun dauki hayar matar daya daga cikin sojojin Najeriya da suke aiki tare kuma ita take dafa masu abinci ta kuma basu ruwan sha.

Sojin Amurka 12 da suka horas da sojin Najeriya sun bayar da labarin zaman su a Jaji
Sojin Amurka 12 da suka horas da sojin Najeriya sun bayar da labarin zaman su a Jaji

Harris kuma ya ce sukan dibo ruwa kamar gallan biyar duk safe sannan suyi wanka a bayin da aka killace da langa-langa. Yadda suke wanka shine suna amfani da bokitin ruwa biyu ne, na farkon su watsa a jinkinsu sannan su goga sabulu sai kuma suyi amfani da bokitin na biyu wajen dauraye jikinsu su.

Kazalika, sojojin sun rubuta cewa gidajen da suka zauna yayi kama da irin gidajen da zaka gani a fina-finan yaki na Hollywood. Akwai gadaje irin na dalibai, kujurun roba da kuma safa aka shanya a kofar gidan kana akwai rubutun da wasu sojojin sukayi a bangon gidajen.

Dukkan su sojoji 12 sunce sunyi matukar farin ciki lokacin da suke koyar da sojojin Najeriyan duk da irin yananyin zafin garin. Shugaban tawagar, Saul Rodriguez yace sun basu horro mai tsanani saboda rayuwarsu ta danganta akan irin abin da suka koya ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164