2019: Idan Buhari bai sake fitowa takarar zabe ba zan maka shi a Kotu - Ganduje

2019: Idan Buhari bai sake fitowa takarar zabe ba zan maka shi a Kotu - Ganduje

- Gwamna Ganduje yace zai maka shugaba Buhari a kotu idan bai sake fito takarar zabe ba

- Gwamnan yace al'umma Najeriya ne da gwamnonin APC ke bukatar Buhari ya tsaya takarar

- Shima gwamna Ganduje ya bayyana niyyar sa na sake tsaya takarar gwamna a zaben 2019

A jiya Juma'a 6 ga watan Afrilu ne Gwamna Umar Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya shaidawa shugaba Buhari cewa zai maka shi a kotu idan har bai sake tsayawa takarar shugabancin kasa ba a zaben 2019.

A hirar da yayi da manema labarai, gwamna Ganduje kuma ya bayyana niyyar sa na sake tsayawa takarar gwamna a jihar Kano a zaben na 2019 domin ya karasa ayyukan da ya faro a jihar ta Kano.

Gwamna Ganduje zai maka Buhari a kotu idan bai fito takarar zaben 2019 ba
Gwamna Ganduje zai maka Buhari a kotu idan bai fito takarar zaben 2019 ba

"Gwamnonin APC suna son shugaba Buhari ya zarce. Nayi farin ciki da cewa ba shugaban kasar bane yace yana son ya zarce, al'umma ne ke son ya sake tsayawa takarar sai dai har yanzu shugaban kasar bai yanke shawara a kan lamarin ba.

DUBA WANNAN: Matasan arewa sunyi gargadi mai tsanani ga Obasanjo kan sukar gwamnatin Buhari

"A wannan kasar, mun ga shugabanin kasar da suka kashe biliyoyin naira don su sake zarce wa kan mulki karo na uku, saboda haka menene matsala idan mutum na son zarcewa karo na biyu kamar yadda kundin tsarin mulki ta bayar da dama?" inji shi.

Ganduje ya kuma bayyana cewa al'ummar jihar Kano ne suka bukace shi ya sake tsayawa takarar.

"Na amince zan sake tsayawa takara karo na biyu kuma al'ummar Kano ma suna son in sake tsayawa amma daga karshe su zasu nuna wa duniya ko na cancanta ko akasin haka."

Da yayi tsokaci kan karin wa'adin mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC, Ganduje ya ce akwai alamu cewa za'a canja matsayar ta a taron da za'a gudanar ranar Litinin domin gwamnonin da suka goyi bayan karin wa'adin yanzu sun gamsu da cewa ya kamata a zabi sabbin yan kwamitin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164