Sakataren gwamnatin tarayya ya bayar da shawara kan yadda za'a magance rashawa a ma'aikatun gwamnati
- Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha bawa hukumar EFCC shawara game da yadda zasu inganta yaki da rashawa
- Sakataren gwamnatin tarayyar yayi kiran ne lokacin da shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya kai masa ziyara a ofishinsa a Abuja
- Mustapha ya bukaci hukumar da tayi amfani da hanyar wayarwa mutane da kai game da illolin cin hanci a cikin aikin gwamnati
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya janyo hankalin hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki kasa ta'annati (EFCC) game da dabarar da zasubi don magance cin hanci da rashawa a kowane mataki na gwamnati.
A ranar Alhamis daraktan labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Lawrence Ojabo, yace sakataren gwamnatin tarayyar yayi kiran ne lokacin da shugaban hukumar kula da tattalin arzikin kasa Ibrahim Magu tare da mutanensa suka kai masa ziyara a ofishinsa.
DUBA WANNAN: Akwai dimbin ayyukan gwamnati shugaba Buhari da ba'a bayyanawa - Oyo-ita
Mustapha ya bukaci hukumar da tayi amfani da hanyar wayarwa mutane da kai game da illolin cin hanci da rashawa a aikin gwamnati. Ya kara cewa komawarsu sabon ofishinsu da ake ginawa a birnin tarayyar zai taimaka masu wurin gudanar da ayyukansu a bincike yadda ya kamata.
Mustapha yayi godiya ga jami’an game da yanda suka karbi kudirin shugaba Muhamadu Buhari na dakile cin hanci kafin ya dakile kasar. Yana tunawa da cewa maganar yaki da cin hanci shine abinda shugaban ya dade yana maimaitawa a lokacin yakin neman zabe.
Magu ya bukaci sakataren gwamnatin da ya kai ziyara a sabuwar Hedikwatar hukumar wadda ake ginawa a birnin tarayyar, Abuja bayan ya masa bayani a kan matsayin da aikin ginin yake inda yace sauran kadan a karasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng