An kama bature da ake zargin shi ya kashe matarsa da 'yarsa a Legas

An kama bature da ake zargin shi ya kashe matarsa da 'yarsa a Legas

- Yan'sanda sun damke wani Dan kasar italia da ya halaka matarsa yar Najeriya da diyarsu a garin Legas

- Mun samu labarin kashe Mawakiya yar kasar najeriya, Zainab Ali_Nielson, wacce akafi sani da Alizee, da kuma yar'ta mai shekaru hudu a duniya, Petra, wadanda mijinta Dan kasar italia mai suna, Peter Nielson ya halaka

- An kashesu ne a gidansu dake ocean parade, Banana Island a safiyar Alhamis

An kama bature da ake zargin shi ya kashe matarsa da 'yarsa a Legas
An kama bature da ake zargin shi ya kashe matarsa da 'yarsa a Legas

An kama bature da ake zargin shi ya kashe matarsa da 'yarsa a Legas
An kama bature da ake zargin shi ya kashe matarsa da 'yarsa a Legas

An kama bature da ake zargin shi ya kashe matarsa da 'yarsa a Legas
An kama bature da ake zargin shi ya kashe matarsa da 'yarsa a Legas

Duk da dai har yanzu bayanin abinda ya faru babu shi dalla dalla, wakilinmu ya tabbatar mana da Peter yana hannun Yan'sanda. Gawarwakin kuma suna mutuware domin binciken sanadin mutuwar tasu.

Mun samu labarin cewa yar'asalin jihar Kogin ta rattaba hannu akan wata yarjejeniya ta shekaru biyu tsakanin ta da Asian record Label da Petra Entertainment a shekara ta 2017, wanda muka samu labarin ya janyo mata samun sabuwar dalleliyar mota kirar Ford Explorer, da kuma gida a Banana Island da kuma mai rarrabawa ta duniya na kamfanin da suka yi yarjejeniyar dake Asia.

DUBA WANNAN: A Zamfara yara 28 ne suka zana jarrabawar shiga sakandare

Mai magana da yawun hukumar yan sanda ta jihar Legas SP Chike Oti, ya tabbatar da kama wanda ake zargi da laifin kisan, yace an tura kungiyar masu binciken gurin da aka aikata laifi gidan.

Yace "kwamishinan yan sanda na jihar, Edgal Imohimi, ya bada damar damke wanda ake tuhuma kuma yana gurin Yan'sanda.

Kwamishinan ya sanar kungiyar binciken su dauko duk wata shaida da suka samu domin yanke hukunci. Hukumar ta tura a rubuce zuwa ga ofishin jakadancin wanda ake zargin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel