Nigerian news All categories All tags
Hukumar Sojin Kasa ta cafke Barayin Shanu 4 a jihar Bauchi

Hukumar Sojin Kasa ta cafke Barayin Shanu 4 a jihar Bauchi

Rahotanni sun bayyana cewa, Dakarun Sojin kasa dake gudanar da atisaye mai taken Lafiya Dole, sun damko wasu barayi 4 na shanu a kauyen Yayari dake karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi tun a ranar 3 ga watan Afrilu na wannan shekara ta 2018.

Hukumar a shafin ta na dandalin sada zumunta ta bayyana sunayen wannan miyagu da ake zargi kamar haka; Musa Muhammad, Magaji Isyaka, Jao Musa da kuma Nura Bello.

Kakakin hukumar Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayyana cewa, a yayin tuntubar wannan mutane da ake zargi sun amsa lafin su da cewar sun yi awon gaba da shanu biyu kuma tuni suka ci kasuwar su a wurin wani Alhaji Ado da ya yi aron kafar Kare.

Barayin Shanu da hukumar Sojin kasa ta cafke a jihar Bauchi

Barayin Shanu da hukumar Sojin kasa ta cafke a jihar Bauchi

Hukumar Sojin ta ci gaba ta baza dakarun ta tare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro domin cafke Alhaji Ado da duk masu hannu cikin wannan kazamiyar sana'a.

KARANTA KUMA: Tinubu ya bayar da sunayen 'yan takara 5 da zasu maye kujerar shugaban jam'iyyar APC

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar Sojin ta ci gaba da sanya idanun lura da karfafa sintiri a yankin da zai hana barayin shanu walwala da kuma sakewa.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, ministan tsaro Birgediya Janar Mansur Dan Ali, ya bayyana adadin dakarun soji da aka dauka aiki cikin shekaru na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel