Najeriya na kashe sama da Tiriliyan 1 wajen tallafin man fetur a karkashin Gwamnatin Buhari

Najeriya na kashe sama da Tiriliyan 1 wajen tallafin man fetur a karkashin Gwamnatin Buhari

Karamin Ministan mai ya bayyana cewa ana biyan tallafin man fetur da sama da Tirilyan guda a shekara yanzu a Najeriya wajen shigo da lita miliyan 50 a kullum inda NNPC tace ana sace man zuwa Nijar, Benin, Kamaru, Chad da Togo.

Mun samu labari daga Jaridar Punch cewa abin da Najeriya ta ke kashewa yanzu wajen biyan tallafin man fetur ya haura Naira Tiriliyan 1.4 bayan a da Shugaba Muhammadu Buhari yayi ikirarin cewa babu wani abu mai kama da tallafin fetur.

Najeriya na kashe sama da Tiriliyan 1 wajen tallafin man fetur a karkashin Gwamnatin Buhari
Shugaba Buhari yana biyan ‘yan kasuwa tallafin fetur

Karamin Ministan mai na kasar Ibe Kachikwu ya bayyanawa manema labarai cewa Hukumar NNPC ne kurum ke jigilar man fetur a kasar don haka ake shan wahalar shigo da mai. Ministan yace za su yi gyara kwanan nan a harkar na man fetur.

KU KARANTA: Zan iya shiga wuta saboda Shugaba Buhari - Gwamna Bello

A watan da ya wuce dama NNPC ta bayyana cewa a duk rana tana kashe Naira Miliyan 774 wajen shigo da mai. A wata dai Najeriya na kashe abin da ya haura Biliyan 20 a tallafin man fetur wanda yanzu dai karamin Ministan mai na kasar ya tabbatar.

Shugaban kamfanin NNPC na kasar Dr. Maikanti Baru ya bayyana cewa wasu na shiga da man Najeriya zuwa kasashen ketare wanda hakan ya sa aka kara yawan fetur din da ake shigowa da shi a kowace rana kuma hakan na iya sa farashi ya tashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng