Sharrin Almajiranci: An tsinci gawar wani Almajiri bayan an farke masa ciki a garin Katsina

Sharrin Almajiranci: An tsinci gawar wani Almajiri bayan an farke masa ciki a garin Katsina

A ranar Talata, 5 ga watan Afrilu ne aka tsinci gawar wani karamin yaro dake almajiranci a jihar Katsina, bayan kwana daya da bacewarsa, aka neme shi sama ko kasa an rasa.

Rariya ta ruwaito wannan yaro mai kimanin shekaru 12 ya dalibi ne a tsangayar Alaramma Abubakar dake da tsangayarsa a unguwar Kwado, a cikin garin Katsina, inda yace a ranar Litinin din data gabata ne dai Almajirin nasa ya bace.

KU KARANTA: Shari’a sabanin hankali: An yanke ma barawon sigari da kwalaben giya hukuncin kisa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Malamin na cewa sun gane yaron baya nan ne a lokacin da yake tambayar almajiransa ko sun dawo tsangaya gabaki daya, kamar yadda ya saba a duk dare, daga nan fa suka dukufa neman yaron, amma har tsakar dare basu same shi ba.

Sai dai washegari, Talata ne daya daga cikin Almajiran tsangayar da suke yawon bara tare da yaron ya dawo yana kuka, inda yace ya ga gawar abokinsa an farke cikinta, kuma an yi masa zarge, alamar kashe shi a aka yi.

Gawar wannan yaro mara gata an tsince ta ne a nan Unguwar Kwadon, bayan dandalin wasanni na jihar Katsina, daga bisani kuma Alaramma Abubakar ya shaida ma Yansanda halin da ake ci, sai dai binciken likitoci ya tabbatar da cewar na’a cire komai a cikin yaron ba.

A wani labarin kuma, wani Malamin almajirai yayi sanadiyyar guntule hannayen wani almajirinsa, bayan ya daure masa hannu na tsawon lokaci kan zargin satar waya, wanda hakan ya sabbaba rubewar hannayen duka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng