Tayar da tarzoma: An garkame mutane 63 a gidan yari a jihar Kaduna

Tayar da tarzoma: An garkame mutane 63 a gidan yari a jihar Kaduna

Wata kotun majistare dake unguwar Daura a garin Kaduna ta kara bayar da umarnin garkame wasu mutane 63 da ake zargi da aikata laifin kisa kai a kasuwar Magani dake jihar Kaduna.

Wadanda ake tuhumar dukkansu mazauna kasuwar maganin, ana tuhumar su da hada baki, zanga-zanga dauke da makamai, yin taron da ya saba da doka aikata kisa tare da tayar da hankula da kuma jefa mutane cikin rudani.

Da aka kira karar a kotun, dan sanda mai gabatar da kara, Inspekta Sunday Baba, ya shaidawa kotun cewar, wadanda ake tuhuma sun amince da kin yin furuci a kotu hat sai sun gama shawara da darektan hukumar gurfanar wa (DPP).

Tayar da tarzoma: An garkame mutane 63 a gidan yari a jihar Kaduna
Gidan yari

Inspekta Baba ya roki kotun da ta bayar da umarnin cigaba da tsare mutanen a gidan yari har sai sun kammala tattaunawa da darektan hukumar DPP.

Mai shari'a, uwargida Zainab Mohammed, ta amince da bukatar Inspekta Baba tare da bayar da umarnin cigaba da tsare su a gidan yari.

Saidai, mai shari'a, Zainab, ta bayar da belin wani yaro mai karancin shekaru dake cikin mutanen sannan ta daga sauraron karar ya zuwa ranar 24 ga watan Afrilu da muke ciki.

DUBA WANNAN: An gurfanar da dan sandan da ya taimakawa masu laifi tserewa daga kurkuku

An gurfanar da mutanen ne bisa zarginsu da hannu a rikicin da ya barke ranar 26 ga watan Fabrairu tsakanin baki da 'yan gargajiya a kan budurwa.

An kone gidaje, shaguna, da kadara ta miliyoyin Naira yayin rikicin. Kazalika rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12.

Har yanzu hukumar 'yan sanda bata yi nasarar kama shugaban kungiyar matasan da ya haddasa rikicin ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng