An bukaci Mantu ya gabatar da shaidar PDP ta aikata magudin zabe a Najeriya
- Wata kungiya ta kallubalanci Ibrahim Mantu ya lissafa sunayen mutanen da suke da hannu cikin magudin zaben da ya ambata anyi
- Kungiyar tayi kira ga mahukunta su gudanar da sahihiyar bincike kan batun don magudin zabe laifi ne da ya sabawa dokar kasa
- Kungiyar kuma tayi kira da mahukunta da al'umma su sa ido sosai don hana magudin musamman yanzu da ake tunkarar zaben 2019
Wata kungiya mai sa'ido kan harkokin da suka shafi musayar mulki 'Transition Monitoring Group' (TMG) ta kallubalance tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu, ya lissafa sunayen ma'aikatan zabe da jami'an tsaro da suka taimaka masa wajen magudin zabe.
A kwanakin nan Mantu ya fadawa duniya cewa ya taimaka wa jam'iyyar PDP wajen yin magudin zabe a baya, wannan zancen nasa ya haifar da cece-kuce sosai a tsakanin yan Najeriya inda har wasu ke bukatar cewa a gurfanar da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan a kotu.
DUBA WANNAN: An mayar da Janga a matsayinsa na kwamishinan 'Yan sanda a jihar Kogi
A wata sanarwa data fitar, shugaban TMG, Dr. Abiola Akiyode-Afolabi tayi matukar mamakin jin wadannan kalaman daga bakin Mantu kuma ta kara da cewa ya kamata hukuma su gudanar da cikaken bincike a kan lamarin saboda yan Najeriya su samu natsuwa bisa irin magudin da aka rika tafkawa bayan sunyi zabe.
Akiyode-Afolabi ta lura cewa wasu na iya cewa abin da Mantu yayi magana a kai ya wuce amma tuba na gaskiya yana bukatar mai laifin ya fuskanci hukuncin da ya dace dashi dai-dai da abin da ya aikata.
Shugabar na TMG ta kuma ce bayar da cin hanci don gurbata sakamakon zabe laifi ne kamar yadda sashi na 124 da 130 na Dokar Zabe na 2010 ya nuna, saboda haka dole ne doka tayi aikin ta.
Daga karshe shugaban Kungiyar tayi kira ga mahukunta da al'umma su bude idanun su sosai lokacin zaben 2019 don har yanzu akwai wadanda basu tuba daga sana'ar magudin zabe ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng