Sun gagari kundila: Wasu manyan matsaloli guda 3 da suka gagari shugaba Buhari

Sun gagari kundila: Wasu manyan matsaloli guda 3 da suka gagari shugaba Buhari

Tun bayan darewar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan madafan iko a shekarar 2015, kimanin shekaru 3 kenan a yanzu, ya yi iya bakin kokarinsa a fannoni daban daban, sai dai akwai matsala fa.

Legit.ng ta ruwaito duk da tsabar soyayyar da Talakawan Najeriya ke nuna ma shugaba Buhari, musamman ma Talakawan Arewa, hakan bai hana su lura da wasu fannoni guda uku da suka ce Buharin ya gaza akansu ba.

KU KARANTA: Uba ya cika wandonsa da iska bayan ya kashe ɗansa sakamakon wata yar saɓani da suka samu

Daga cikin wadannan gagaruman matsaloli guda uku, akwai:

1- Tsaro: Babu shakka du wani mai bibiyan al’amuran yau da kullum a kasar Najeriya zai tabbatar da cewar dakarun Sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun yi iya bakin kokarinsu wajen yaki da Boko Haram, inda a yanzu haka sun dakatar da ayyukan kungiyar ta’addancin a yankin Arewa maso gabas kadai.

Sai dai fa ba anan gizo ke sakar ba, tunda har yanzu Boko Haram ta nuna tana da karfin satar mutane da dama, kamar yadda suka yi a kwalejin yan mata dake garin Dapchi na jihar Yobe, inda suka saci yan mata 110, baya da hare hare da suka kaiwa na kunar bakin waje a Garejin Muna dake jihar Borno.

Hakazalika, wata sabuwar matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewacin kasar nan itace ta barayin shanu yan bindiga da suke cin karensu babu babbaka a jihohin Zamfara, Katsina da yankin Kaduna, inda suke karkashe mutane ba tare da la’akari da addininsu ko kabilarsu ba, wanda hakan yayi sanadiyyar tashin kauyuka da dama, duk da cewa an kashe shugabansu, Buharin Daji.

2- Man Fetir: Sanannen abu ne ga duk dan Najeriya da ya yi tsawon shekaru a kasar cewa a duk karshen shekara ana samun matsananciyar karancin man fetir a kasar, wanda hakan ke tsawwala kudin mota, farashin kayan abinci su yi tashi gwauron zabi, sanadiyyar hakan rayuwa na kuntata.

Kamar da gaske, shekaru biyu cikin gwamnatin Buhari ba’a samu matsalar ba, amma sai gashi a karshe shekarar 2017 an shiga mawuyacin hali a sakamakon karancin man fetir din, wanda ya kai har watan Maris na shekarar 2018.

Babban abin dake daure kai game da wannan batu shine duk da matatun mai a Najeriya, kamfanoni masu zama kansu da kuma shigo da mai da ake yi daga kasashen waje, amma duk da haka matsalar ta gagari kundila.

3- Rikicin cikin gida a APC: Wata matsala da ta ki ci, ta ki cinyewa da Buhari ya sanya ma idanu, it ace matsalar rikita rikitan cikin gida da ta dabaibaye jam’iyyar APC. Yawancin matsalolin nan sun fi gawurta a jihohin Arewa, inda jam’iyyar ta fi samun tagomashi da gwamnoni 17.

Da dama daga cikin rikita rikitan nan suna samo tushensu ne daga sabani tsakanin gwamnan jiha da wasu Sanatocin da suka fito daga jihar, kamar Kaduna, Kano, Bauchi da Sakkwato. Sai dai a yayin da suke kara ruruwa, shugaba Buhari ya nuna baya iya magancesu, abinda jama’a ke tambaya a nan shi ne “APC zata kai bantenta a haka?”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng