An mayar da Janga a matsayinsa na kwamishinan 'Yan sanda a jihar Kogi
- Shugaban ‘Yan Sanda ya mayar da Ali Janga a matsayinsa na kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kogi
- Janga ya koma bakin aikinsa a ranar Alhamis bisa ga umurnin Sifeta janar na ‘Yan Sanda Ibrahim Idris
- Janga yace an mayar dashi bakin aikinsa bayan ya cika sharadin kamo wadanda suka tsere daga hannun yan sandan cikin mako daya
Shugaban Jami’an ‘Yan Sanda Ibrahim Idris, ya mayar da Ali Janga a matsayinsa na kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kogi. Mai magana da yawun hukumar ASP William Aya ne ya tabbatar da zancen.
Aya ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran kasa (NAN) cewa Janga ya koma bakin aikinsa a ranar Alhamis, 3 ga watan Afirilu, a garin Lokoja, bisa ga umurnin shugaban hukumar ta ‘Yan Sanda Ibrahim Idris.
DUBA WANNAN: Kotu ta yankewa shahararen jarumin Bollywood shekara 5 a gidan yari
Janga yace an mayar dashi bakin aikinsa bayan ganawar da sukayi da shugaban hukumar akan wa’adin sati daya da ya bashi akan ya gano wadanda suka gudu daga hannun hukumar a jihar.
ASP William ya tabbatar da cewa duka mutane shidan da suka gudu daga hannun hukumar a ranar 28 ga watan Maris an kamosu. Ya kara da cewa mutane 13 wadanda suke da hannu a guduwar wadancan suma an kamasu a Lokoja.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng