Kuyi watsi da 'yan adawa masu bakar aniya: Fadar shugaban kasa ta shawarci 'yan Najeriya
- Fadar shugaban kasa ta ahwarci 'yan Najeriya suyi kunnen uwar shegu da yan adawa masu mumunar aniya
- Malam Garba Shehu babban mataimakin shugaba Buhari ta fannin sadarwa ya bayyana haka a wani jawabi da yayi a Abuja
- Shehu yace gwamnatin tarayya na nan tana aiki tukuru don ganin cewa kowane dan Najeriya yaga canjin daya zaba a shekarar 2015
Fadar shugaban kasa ta shwarci ‘yan Najeriya dasu rinka tunowa da cigaban tattalin arziki da gwamnatin Buhari ya kawo kadasu saurari zantuttukan ‘yan adawa, don basa son cigaban kasa.
DUBA WANNAN: EFCC zata fara bincike akan 'yan PDP da aka lissafo sunayen su a jerin sunayen barayin gwamnati
Malam Garba Shehu babban mataimakin shugaba Buhari ta fannin sadarwa ya bayyana haka a wani jawabin da yayi ranar Laraba a birnin tarayya.
Shehu yace gwamnatin tarayya na nan tana aiki tukuru don ganin cewa kowane dan Najeriya yaga canjin daya zaba a shekarar 2015.
Daya daga cikin jami’an Shugaban kasa lokacin da yake lissafa cigaban da shugabaBuhari ya kawo, ya tuna da lokacinda Bankin duniya ya sanya Najeriya a matsayi na 10 cikin kasashe masu tattalin arziki a shekarar 2007.
Shehu yace an samu cigaba da dama a wannan gwamnati ta yanda kudin gangar mai ya karu da kuma yawan shigowa da abinci ya ragu sakamakon gigaba da aka samu ta fannin noma, sannan wutar lantarki ta kara samu a kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng