Mutane 3 sun kone kurmus yayinda wata mota ta kama da wuta a hanyar Abuja

Mutane 3 sun kone kurmus yayinda wata mota ta kama da wuta a hanyar Abuja

- Wasu mutane uku sun kone kurmus har lahira yayinda motar su ta kama da wuta a kauyen Sabon Gari dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja. Wani wanda hadarin ya faru a gaban shi ya bayyanawa manema labarai cewar, lamarin ya faru ne a ranar Litinin dinnan da misalin karfe 3:13 na dare, yayinda wata mota kirar J5 mai lamba JKA 567XF ta fada cikin wani rami sannan ta kama da wuta a take a wurin

Mutane 3 sun kone kurmus yayinda wata mota ta kama da wuta a hanyar Abuja

Mutane 3 sun kone kurmus yayinda wata mota ta kama da wuta a hanyar Abuja

Wasu mutane uku sun kone kurmus har lahira yayinda motar su ta kama da wuta a kauyen Sabon Gari dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja. Wani wanda hadarin ya faru a gaban shi ya bayyanawa manema labarai cewar, lamarin ya faru ne a ranar Litinin dinnan da misalin karfe 3:13 na dare, yayinda wata mota kirar J5 mai lamba JKA 567XF ta fada cikin wani rami sannan ta kama da wuta a take a wurin.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP ta nuna goyon bayanta akan sake salon zabe

Ya ce direban motar da wasu fasinjoji guda biyu sun kama da wuta sun kone kafin wani ya kawo musu taimako, sannan ya kara da cewar sai daga baya jami'an hukumar kiyaye hadura na kasa suka zo suka fitar da gawarwakin.

A lokacin da aka tuntube shi, Kwamandan hukumar kiyaye haduran na yankin (ACC) Joseph Samgbaza, ya tabbatar da faruwar hadarin, inda ya danganta hadarin da gudu da direban yake yi wanda ya wuce misali. Sannan ya bayyana cewar hukumar ta mika gawarwakin mutanen ga iyalan su dake Lokoja.

Har ila yau, majiyar Legit.ng ta kara samo rahoton cewar, wasu mutane uku sunji rauni a wani hadarin daya faru a ranar Litinin dinnan data gabata a kusa da kauyen Gwako dake kan hanyar Gwagwalada zuwa Zuba. Inda aka tabbatar da cewar hadarin ya faru ne yayinda wata mota mai kirar Golf marar number ta kwace daga hannun direban ta daki wani gini, inda mutane uku suka ji ciwo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel