Tattalin arziki: Babban bankin Najeriya CBN ya gargadi Shugaba Buhari

Tattalin arziki: Babban bankin Najeriya CBN ya gargadi Shugaba Buhari

- CBN ta nemi Gwamnatin Najeriya ta adana rarar kudin ta

- Kwanaki farashin danyen mai ya tashi a kasuwannin Duniya

- Akwai bukatar a ajiye kudi kafin darajar mai ya kara sauka

Babban Bankin Najeriya watau CBN ya ja kunnen Gwamnatocin Najeriya da su bi a sannu ganin yadda gangar mai yake kudi yanzu a Duniya bayan a baya farashin sa ya karye a kasuwannin Duniya.

Tattalin arziki: Babban bankin Najeriya CBN ya gargadi Shugaba Buhari
Gwamnan CBN ya nemi Shugaba Buhari ya adana dukiyar kasa

Bankin kasar na CBN ya gargadi Gwamnatin Tarayya da ma na Jihohi da Kananun Hukumomi da su adana rarar kudin da su ka samu saboda gobe. Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ne ya bayyana wannan bayan wani taro.

KU KARANTA: Osinbajo na nema kowa ya samu inshorar rashin lafiya

A wannan makon ne CBN tayi taron ta na MPC na 260 inda ta ba Gwamnati shawarar adana kudin da ta samu bayan fetur yayi tsada domin kuwa da alama cewa farashin man fetur da Najeriya ta dogara da shi zai kuma karyewa kwanan nan.

CBN tayi wannan gargadin ne ganin yadda Najeriya ta samu kan ta cikin matsi kwanaki bayan da tattalin arzikin kasar ya ruguje bayan fetur ya karye a kasuwa. Gwamnan ya kuma bayyana cewa Najeriya na da Dala Biliyan 46.699 a asusun waje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng