Tsohon mataimakin shugaban kasa, tsohon gwamna kuma Sanata ya shiga zawarcin mukamin gwamna a Filato

Tsohon mataimakin shugaban kasa, tsohon gwamna kuma Sanata ya shiga zawarcin mukamin gwamna a Filato

Wani tsohon gwamnan jihar Bendel, wato jihohin Edo da Delta a yanzu, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa a zamanin mulkin Soja, na marigayi janar Sani Abacha, Sanata Jeremiah Useini ya kaddamar da takararsa ta kujerar gwamnan jihr Filato

The Cables ta ruwaito Jeremiah mai shekaru 74, wanda a yanzu haka shi ne wakilin al’ummar jihar Filato ta kudu a majalisar dattawa, ma’ana Sanata ne a yanzu, ya taba zama gwamnan jihar Bendel kimanin shekaru 34 da suka gabata.

KU KARANTA:Uba ya cika wandonsa da iska bayan ya kashe ɗansa sakamakon wata yar saɓani da suka samu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ya bayyana aniyarsa ta taka takarar gwamnan jihar Filato ne a ranar Laraba 4 ga watan Afrilu a babban ofishin jam’iyya PDP dake Jos, da nufin gwada kwanji da gwamnan jihar, Simon Lalong mai shirin yin tazarce.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, tsohon gwamna kuma Sanata ya shiga zawarcin mukamin gwamna a Filato
Useni

A kwanakin baya ma Sanatan ya aika ma wani dan majalisa daya fito daga jihar, Timothy Golu wasikar neman goyon baya daga gare shi, nda ya bayyana manufarsa ta tsayawa takara ita ce burin samar da dawwamammen zaman lafiya da adalci a Filato.

“Ina son dawo da zaman lafiya da adalci a Filato, ina son dawo da so da kaunar juna da aka sanmu da shi, ina son dawo da martaba da mutuncin jihar Filato a idon Duniya, Filato ta mu ce, don haka ya zama wajibi mu daukaka ta.” Inji shi.

Shugaban kwamitin yakin neman zabe na Jeremiah Useni, Dimis Mailafia yace jiharsu na bukatar kwararren hannu kuma wanda ya san makamar aiki don daurata akan turbar cigaba mai daurewa.

Da wannan zaben shekarar 2019 dake karatowa, muddin burin Jeremiah Useni ya tabbata, zai zamo gwamna mafi yawan shekaru a Najeriya, inda a lokacin shekarunsa zasu kai 75.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng